Bukayo Saka zai yi jinyar makonni 'masu yawa' - Arteta

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Sean Kearns
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 1
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ɗanwasan gaba Bukayo Saka ba zai buga wasa tsawon "makonni masu yawa" saboda rauni a bayan gwiwarsa.
An fitar da ɗanwasan na Ingila a wasan da Arsenal ta doke Crystal Palace 5-1, inda ya bar filin wasa na Selhurst Park da sanduna.
Saka mai shekara 23 ya ci wa Arsenal ƙwallo tara kuma ya bayar aka ci 13 cikin wasa 24 da hya buga mata a dukkan gasanni.
"Lamarin babu kyau," in ji Arteta. "Zai yi jinyar makonni masu yawa.
"Haka dai lamarin yake. Ya ji rauni, ba zamu iya sauya komai ba. Za mu yi amfani da wannan lokacin domin taimaka masa."
Arteta ya ce yana "tunanin ɓullo wa lamarin" domin magance matsalar rashin Saka kuma da ma Arsenal ta saba buga wasa ba tare da manyan 'yanwasanta ba kamar kyaftin Martin Odegaard a kakar nan.
Koci ya ƙara da cewa Saka ya "kaɗu" kuma ya "shiga wani yanayi" bayan gano haƙiƙanin girman raunin.
Da aka tambaye shi ko yawan wasanni na cikin dalilan da suka jawo raunin, Arteta ya ce: "Babu mamaki yawan wasannin ne saboda Saka da Rice sun buga wasanni sama da 130 a kaka uku."
Ya kuma tabbatar cewa FRaheem Sterling ma zai yi jinya saboda rauni a ƙafa.
Arsenal za ta buga wasa na gaba da Ipswich ranar 27 ga watan Disamba a filin wasa na Emirates.











