Ba mu da zaƙaƙuran 'yangaba da za su fitar da mu kunya - Arteta

Asalin hoton, OTHERS
Bisa ga dukkan alamu fatan Arsenal na cin kofin Premier bana kusan a ce ya ƙare ko da kuwa kociyanta Mikel Arteta ba zai fito fili ya yarda da hakan ba.
Ƙungiyar da take ta biyu a tebur da tazarar maki 13 tsakaninta da jagaba - Liverpool, bayan ta yi canjaras ba ci a gidan Nottingham Forest, hakan ya ƙara taso da maganar cewa Gunners ɗin ba su da wadatattun 'yangaba da za su fitar da su kunya a ranar neman wanda zai cire mata kitse a wuta.
A wasansu biyu na baya na Premier, Arsenal ɗin ta kai hari 33, to amma uku ne kawai suka hari raga daidai amma kuma duk da hakan ma ba wanda nifi ya cika -ƙwallon ta shiga raga.
Wannan shi ne karon farko tun watan Mayu na 2023 da Gunners ɗin suka kasa zura ƙwallo a raga a wasannin Premier a jere inda aka tilasta mayar da Mikel Merino ya je gaba saboda rashin 'yangaban.
Arteta ya ce: "Mun mamaye wasan. Mun yi ƙoƙari ta fannoni da dama. Mun kafe amma ba mu da wannan karsashin da ake buƙata a ƙarshe da zai keta gwanayen 'yanwasa. Dole ne mu riƙa kai hari daidai ba ƙakƙautawa."
Duk da cewa jinyar 'yanwasan gaban Arsenal ɗin irin su Gabriel Jesus, Bukayo Saka, Gabriel Martinelli da Kai Havertz, ta haifar musu da cikas, akwai shakku kaɗan cewa ƙungiyar za ta ƙara tashi tsaye wajen neman mai ci mata ƙwallo a bazara.
Tsohon mai tsaron ragar Gunners ɗin David Seaman, shi ma yana ganin hakan a wata tattaunawa da ya yi da BBC : "A kodayaushe muna buƙatar ɗangaba. Mun yi ƙoƙari a lokacin kasuwar da ta gabata kuma yanzu ma muna sa ran haka a lokacin bazara to amma zuwa wannan lokacin zai iya zama mun ɗan makara.
"Wannan shi ne abin da muke buƙata. Wannan ƙila shi muke fatan zai faru a kaka mai zuwa." In ji tsohon golan na Arsenal.
To amma yadda su ma abokan hamayyar Arsenal ɗin a Premier kamar su Manchester United, da Chelsea, da Tottenham, da kuma Aston Villa za su iya fita neman ɗangaba a bazara, zai yi wuya sosai Arsenal ta samu wannan tauraron ɗangaba da take buƙata.











