Ina aka kwana a alƙawuran da aka yi wa mutanen Tudun Biri?

Asalin hoton, UBA SANI
Wata guda kenan cif cif da aukuwar harin bama-bamai ta sama ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuki, wanda aka bayyana cewa na kuskure ne, a kauyen Tudun Biri na yankin karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, yayin da al'ummar kauyen da na Ugara da Sabon Gida suke gudanar da taron maulidi.
Al'amarin ya yi sanadin asarar rayuka fiye da 100, wasu da dama kuma suka tsira da munanan raunuka, bayan ga asarar kadarori.
Har yanzu kuma mutanen kauyen na Tudun Biri suna jiran a cika alkawuran da aka yi masu na taimaka masu ta fuskoki daban-daban.
Bayan aukuwar abin kaicon a kauyen Tudun Biri na jihar Kaduna, a ranar 3 ga watan Disamban da ya gabata, an yi alkawura da dama ga mutanen kauyukan da abin ya shafa.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana aniyar sake gina kauyen da harin ya ragargaza, ta hanyar gina masu gina gidaje da asibitoci da makarantu da hanyoyi da dai sauransu.
Su ma gwamnonin arewacin Najeriya sun bayar da gudunmawar kudi naira miliyan dari da tamanin, yayin da 'yan majalisar wakilan Najeriya na arewacin kasar suka bayar da naira miliyan arba'in da biyar, da alkawarin samar da wasu ayyukan raya kasa. Sannan majalisar dattawan Najeriya ita ma ta bayar da tata gudunmawar ta naira miliyan dari da tara.
Ina aka kwana ?
Idris Dahiru, wani wanda ya rasa mutum talatin da hudu a cikin danginsa a yayin harin na Tudun Biri, ya ce har yanzu suna cikin jimami.
Ya ce ''Gwamna da kansa yana ziyartar 'yan uwanmu da aka tsugunar a Kaduna, ya bayyana mana cewa ba ya son mayar da mutane wannan wuri yanzu sai an kammala komi an mana gine-gine''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ara da cewa ''Har gwamna ya tura gireda an je an share hanyar wurin, kuma ya kafa kwamiti domin bibiyar alkawuran da aka yi mana domin ganin an cika su''
Shima Shu'aibu Sulaiman, mai unguwar Tudun Biri, ya ce 'Alkawarin da aka mana har yanzu dai muna nan muna sa ido, mutanenmu wadanda ke asibiti suna samun kulawa ba laifi, sannan an kawo mana gudummawar abinci, gwamnatin jiha ma ta kawo ita ma gwamnatin tarayya ta kawo''
Dangane da wannan batu BBC Hausa ta tuntubi kakakin gwamnatin jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, inda ya ce ba shakka gwamnatin jihar ta kafa kwamiti karkashin mataimakiyar gwamnan jihar domin tattara bayanai da kudaden da aka samu.
''Cikin kwamitin har da wakilan mutanen Tudun Biri, da na gwamnatin jihar da sauransu, kuma abun da ake so a yi shine tabbatar da ganin cewa mutanen sun amfana kai tsaye da tsarin da aka yi masu'' in ji kakakin gwamnan.
Yayin da aka cika wata guda da faruwar wannan al'amari, mutane da dama sun zuba ido su ga ko za a cika alkawuran da a aka yi wa mutanen da har yanzu, ke jimamin wannan al'amari da ya rutsa da su.










