Boniface ba zai buga wa Super Eagles Afcon ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Bayer Leverkusen, Victor Boniface, ba zai buga wa Najeriya gasar Kofin Afirka ba sakamakon rauni.
Wannan koma-baya ne ga Super Eaglees, wadda take fatan daukar kofin babbar gasar tamaula ta Afirka karo na hudu jimilla.
Mai shekara 23, shi ne na baya-bayan nan da ya ji rauni a tawagar Najeriya da take cikin wadanda za su fafata a gasar da za a fara ranar 113 ga watan Janairu a Abidjan.
An kira dan kwallon Nice, Terem Moffi, domin maye gurbin Boniface, yayin da ake jiran amincewar hukumar kwallon kafar Afirka da kuma kungiyar da ke buga Ligue 1.
Boniface ya shiga jerin ƴan wasan Najeriya da suka hakura da buga Afcon a bana, sakamakon rauni da suka hada da mai taka leda a Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi, da na Leicester City, Wilfred Ndidi.
Sai dai ana sa ran Kelechi Iheanacho, mai taka leda a Leicester City wanda bai samu halartar sansanin Super Eagles ba, zai je sansanin tawagar kafin ta nufi Ivory Coast.
Boniface yana kan ganiya a kungiyar Jamus, wanda ya ci kwallo 10 ya kuma bayar da bakwai aka zura a raga a Bundesliga a kakar nan.
Ya ji raunin ne a wasan sada zumunta a Abu Dhabi da Super Eagles ta yi rashin nasara 2-0 a hannun Guinea ranar Litinin.
Najeriya tana rukunin farko a gasar Kofin Afirka da za ta fara wasa ranar 14 ga watan Janairu.
Haka kuma Super Eagles za ta fuskanci mai masukin baki Ivory Coast da kuma Guinea-Bissau a dai rukunin farkon.











