Greenwood zai koma Marseille daga Man United

Mason Greenwood

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mason Greenwood zai je Marseille, domin a auna koshin lafiyarsa a shirin komawa ƙungiyar da taka leda daga Manchester United.

Wata majiyar ta ce Greenwoord ya amince da ƙunshin yarjejeniyar da Marseille ta gabatar masa har da karin tsarabe-tsarabe da zai kai £25.2m zuwa karshen 2029.

Magajin garin birnin Marseille ya soki shirin ƙungiyar na sayen ɗan wasan a makon jiya.

Duk da hakan bai hana Marseille cinikin Greewood ba, wanda ake sa ran zai yi aiki karkashin koci, Roberto de Zerbi daga kakar da za a fara ta bana.

Rabonda Greenwood ya yi wa United tamaula tun 2022, bayan da aka tuhume shi da yunkurin fyaɗe da cin zarafi, daga baya aka wanke shi a Fabrairun 2023.

Wata majiya daga United ta ce ɗan wasan mai shekara 22 ya tattauna da shugabannin ƙungiyar, waɗanda suka sanar masa cewar za su sayar da shi.

Greenwood shi ne zai maye gurbin Pierre-Emerick Aubameyang, wanda ya sanar a kafarsa ta sada zumunta zai bar buga gasar Ligue 1.

Tsohon ɗan wasan Arsenal, mai shekara 35, wanda ya taka leda a Chelsea, zai koma yin tamaula a Al-Qadisiyah ta Saudi Arabia.