Man United ta sanar da ƴan wasa 25 da za su kara da Rosenborg

Asalin hoton, Getty Images
Erik ten Hag ya bayyana ƴan wasa 25 da Manchester United za ta je ta buga wasan sada zumunta da Rosenborg ranar Litinin.
Wasu daga manyan ƴan kwallon ƙungiyar sun koma sansanin horon United da ke Carrington tun daga karshen mako, domin shirin tunkarar kakar 2024/25.
Da yake wasu ƴan wasan United na can suna buga wa kasarsu Euro 2024 ko sun kara a Copa America da masu yin hutu, tuni ta kira wasu matasan daga karamar ƙungiyar.
United za ta buga wasan sada zumuntar a Trondheim a Norway ranar Litinin.
Ƙungiyar Old Trafford za ta kece raini da Rosenborg a Lerkendal Stadium daga nan za ta je Amurka, domin buga wasannin shirin tunkarar kakar bana.
Tuni United ta bar Ingila ranar Lahadi da sanyin safe tare da ƴan wasa 25 da za su buga mata karawar, sannan ta ziyarci Amurka.
Harry Maguire yana atisaye shi kaɗai a Carrington, bayan jinya da ya sha.
Andre Onana da Victor Lindelof da Amad da Antony da kuma Jadon Sancho duk suna ta yin atisaye don komawa kan ganiya.
Ƴan wasa 25 da United za ta buga wasannin sada zumunta
Masu tsare baya
- Elyh Harrison
- Dermot Mee
- Radek Vitek
Masu tsare baya
- Harry Amass
- Sonny Aljofree
- Rhys Bennett
- Jonny Evans
- Will Fish
- Louis Jackson
- Sam Murray
- Habeeb Ogunneye
- Maximillian Oyedele
- Aaron Wan-Bissaka
Masu buga tsakiya
- Casemiro
- Toby Collyer
- Jack Fletcher
- Hannibal
- Samuel Mather
- Mason Mount
- James Scanlon
- Ethan Williams
Masu cin ƙwallaye
- Ethan Ennis
- Joe Hugill
- Marcus Rashford
- Ethan Wheatley












