Madrid ta ajiye wa Mbappe lamba 10, Chelsea za ta biya fam miliyan 111 kan Osimhen

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Manchester United da Ingila mai shekara 26 Marcus Rashford na sahun gaba cikin jerin waɗanda Paris St-Germain ke son maye gurbin Kylian Mbappe, da ke shirin raba gari da ƙungiyar ta Faransa a ƙarshen kaka. (Times - subscription required)
Real Madrid ta adana wa Mbappe lamba 10 idan har ya zo ƙungiyar daga Paris St-Germain a bazara. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Shugaban ƙungiyar Florentino Perez ya shaida wa ƴanwasan Real Madrid cewa Mbappe zai zo ƙungiyar a karshen kaka. (Footmercato - in French)
AC Milan za ta buƙaci ƙarin kuɗi yuro miliyan 100 kan ɗanwasanta na gaba mai shekara 24 Rafael Leao, wanda shi ma ake alaƙantawa da Paris St-Germain domin maye gurbin Mbappe. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester City na fatan tafiyar Mbappe Real Madrid sa ɗanwasanta na gaba Erling Haaland ya sabunta kwangilar shi har zuwa 2029. (Mirror)
Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 111 domin karɓo ɗanwasan gaba na Napoli da Najeriya Victor Osimhen. (Rudy Galetti)
Manchester United na son matashin ɗanwasan gaba na Bayern Munich mai shekara 18 Mathys Tel. (Sky Sports)
Newcastle da Aston Villa na ribibin ɗanwasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe. (Football Insider)
Daraktan ƙwallon kafa na Newcastle Dan Ashworth, da Manchester United ta tuntuɓa zai kawo Kyle Macaulay na Chelsea idan har ya koma aiki a Old Trafford. (Sun)
Koci Oliver Glasner zai jagoranci atisayen Crystal Palace karon farko a ranar Talata bayan tabbatar da shi a matsayin wanda zai gaji oy Hodgson. (Fabrizio Romano)
Bayer Leverkusen na farautar ɗanwasan bayana na Luton da Ingila mai shekara 21 Teden Mengi. (Mirror)
Galatasaray na tunanin ɗauko golan Manchester United da Turkiyya mai shekara 25Altay Bayindir, wanda sau ɗaya kawai ya haska tun zuwansa daga Fenerbahce. (A Spor via Teamtalk)











