Udinese ta bai wa Cannavaro aikin koci zuwa karshen kakar nan

Asalin hoton, Getty Images
Udinese ta nada tsohon mai tsaron bayan tawagar Italy, Fabio Cannavaro a makin koci zuwa karshen kakar nan.
Cannavaro wanda ya dauki kofin duniya a 2006 a matsatin kyaftin din Italy, ya maye gurbin Gabriele Cioffi, wanda aka kora bayan da Verona ta ci 1-0.
Hakan ne ya sa Udinese ta kara yin kasa zuwa ta 17 a kasan teburin Serie A - maki daya tsakani da 'yan ukun karshen teburi da maki 28 iri daya da na Frosinone ta 18.
Cannavaro ya saka hannu kan kunshin kwantiragin da zai kare a kungiyar zuwa karshen Yunin bana.
Shi ne zai ja ragamar kungiyar a karashen minti 18 da Roma ranar Alhamis a gasar Serie A.
Tun a baya kungiyoyin sun fafata a gasar, inda aka soke karawar ana 1-1, bayan da dan kwallon Roma, Evan Ndicka ya fadi a cikin fili.
Dan kwallon tawagar Ivory Coast ya farfado a asibiti daga nan aka sallame shi, Roma ta ce mai shekara 24 ya gamu da ciwon kirji, amma ba cutar bugun zuciya bace.
Cannavaro zakakurin mai tsaron baya ne a lokacin da yake taka leda, wanda ya lashe Ballon d'Or a 2006, wanda ya taka leda a Parma da Juventus da Inter Milan da kuma Real Madrid.
Ya yi ritaya a 2011 daga nan ya fada sana'ar horar da tamaula, wanda ya koma nahiyar Asia.
Cannavaro ya horar da kungiyoyi a China da Saudi Arabia, ya kuma yi wata shida a matakin kociyan tawagar China a 2019 daga nan ya horar da Benevento.
.










