Raya ya lashe kyautar safar hannu ta zinare a Premier

David Raya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya lashe kyautar safar hannu ta zinare a matakin wanda ya yi wasa da yawa kwallo bai shiga ragarsa ba a Premier League.

Hakan ya biyo bayan da Luton Town ta zira kwallo a ragar golan Everton, Jordan Pickford ranar Juma'a a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

Tun daga ranar Juma'ar Raya ya yi wasa 14 a karawa 29, kwallo bai shiga ragarsa ba a bana, wanda ke buga wasannin aro daga Brentford.

Ranar Asabar Arsenal ta doke Bournemouth 3-0 a wasan mako na 36, kuma Raya ne ta tsare raga, kenan ya yi karawa 15 ba tare da kwallo ya shiga raga ba.

Kafin wasan Everton ranar Juma'a, Pickford shi ne ake ganin zai iya tarar da golan Arsenal, Raya a matakin lashe kyautar safar hannu ta zinare a Premier League.

Ranar Juma'a Luton da Everton suka tashi 1-1 , inda Elijah Adebayor ya farke kwallon da aka ci Luton, hakan ya sa Raya ya lashe kyautar da ake bai wa golan da ya yi wasa da yawa kwallo bai shiga ragarsa ba.

Tun bayan da Raya ya zama mai tsaron ragar Arsenal a cikin Satumba, wasa biyu ne kadai bai yi ba a Premier, shi ne da Brentford, wadda ta bayar da aronsa ga Gunners.

Aaron Ramsdale ne ya buga wasa biyu da Brentford, inda Gunners ta ci 1-0 a wasan farko da cin 2-1 a karawa ta biyu.