Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum hudu sun mutu a gobarar fitaccen gidan yarin Iran
Kafar yada labaran kasar Iran ta ce fursunoni hudu ne suka mutu, sannan kuma 61 suka ji raunuka bayan gobara ta tashi a fitaccen gidan yarin Evin da ke kasar Iran.
Wata majiya daga gidan yarin - wanda ake daure fursunonin siyasa a kasar - ta shaida wa BBC cewa adadin wadanda abin ya rutsa da su ya zarta haka.
Bidiyon da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna yadda hayaki ya turnuke saman gidan yarin da ke birnin Tehran, an kuma ji karar harbin bindiga da abubuwan fashewa.
A 'yan makonnin nan dai kasar na fama da masu zanga-zangar adawa da gwamnati.
Wadda ta faro cikin watan da ya gabata bayan mutuwar wata matashiya mai suna Mahsa Amini a hannun jami'an 'yan sanda. Jami'ai sun ce ta mutu ne sakamakon bugun zuciya, to amma danginta sun karyata ikirarin, suna masu cewa ta mutu ne sakamakon dukan da 'yan sanda suka yi mata.
Wakiliyar BBC ta ce kawo yanzu dai babu masaniya game da cewa ko tashin gobarar na da alaka da zanga-zangar.
kafafen yada labaran kasar sun ce tashin gobarar ba shi da alaka da zanga-zangar, inda ta ambato wani jami'i na dora alhakin tashin gobarar kan abin da ya kira 'ayyukan miyagu'.
Yayin da yake magana ga gidan talbijin na kasar, Gwamnan Tehran ya ce an samu miyagun da suka gudanar da bore a gefen gidan yarin.
Wasu 'yan jarida a shafukan sada zumunta sun zargi hukumomin kasar da shirya gobarar da gayya, domin kuwa a cewarsu sai da aka saki dan gidan tsohon shugaban kasar da ke tsare a gidan yarin kafin gobarar ta tashi.
A 'yan kwanakin nan ne dai aka saki Mehdi Hashemi Rafsanjani, dan gidan tsohon shugaban kasar Akbar Hashemi Rafsanjani kamar yadda dan uwansa ya fada
An fara yada bidiyon gobarar a shafukan sada zumunta da yammacin ranar Asabar.
A bidiyoyin gabarar da aka yada an yi ta jin muryoyin mutane da ke wajen gidan yarin na ta rera wakokin da ke cewa ''Allah ya la'anci mai kama-karya''.
Daya daga cikin manyan kirarin zanga-zangar adawa da gwamnatin.
An dai hana 'yan uwa da lauyoyin fursunonin kusantar gidan yarin yayin da gobarar tashi da yammacin ranar Asabar, an kuma rufe titunan da ke kai wa ga gidan yarin, kamar yadda 'yan uwan wani fursunan siyasa da ke gidan suka shaida wa BBC.
Wasu 'yan uwan wani fursunan kuma sun ce ba su samu dan uwan nasu a waya ba, a yayin da aka katse hanyoyin intanet da ke gidan yarin.
To sai dai daga baya an bar wasu fursuninin sun gana da iyalansu, tare da shaida musu cewa ba sa cikin hatsari.
Niloufar Hamed wata 'yar jarida ce wadda mijinta ke tsare a gidana yarin, ta kuma samu damar samunsa a waya, inda ya shaida mata cewa yana cikin koshin lafiya, bai ma san abin da ke faruwa a gidan yarin ba.
A Ranar Asabar da daddare gidan Talabijin na kasar ya nuna yadda wasu sassa na gidan yarin ke cikin kwanciyar hankali. To amma wani dan jaridar kasar Masoud Kazemi da a yanzu ke gudun hijira, wanda kuma ya shafe lokaci mai tsawo tsare a gidan yarin ya ce, rahoton gidan talbijin din ya nuna wuraren kawai da gobarar ba ta shafa ba ne.
A gidan yarin ne dai ake tsare da fitattun masu fafutikar nan wadanda ke da izinin zama 'yan Birtaniya da Iran Nazanin Zaghari-Ratcliffe da Anoosheh Ashoori, kusan shekaru masu yawa kan zarge-zargen leken asiri, zargin da suka sha musantawa, kafin a sake su a farkon wannan shekara.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasashen yamma dai sun dade suna sukar gidan yarin, wanda suke zargin hukumominsa da amfani da barazana, da azabtar da fursunonin da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma rashin wadatattun magunguna ga fursunoni.
Wasu gwamnatocin kasashen waje wadanda 'yan kasarsu ke tsare a gidan yarin sun fara bayyana damuwa .
Mai magan da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce yana biye da lamarin cikin ''gaggawa'', yayin da ministan tsaron Birtaniya ya kira lamarin da ''abu mai matukar tayar da hankali''.
Tun bayan mutuwar Misis Amini makonni biyar da suka wuce, zanga-zanga ke ci gaba da barkewa a sassa daban-daban na kasar, wadanda ke kalubalantar jamhuriyar musulunci tun kafuwarta a shekarar 1979.
Zanga-zangar dai ta yi ajalin mutane da dama wadanda mafiya yawansu matsana ne