Arsenal ta tsawaita zaman Elneny a Emirates zuwa 2024

Mohamed Elneny

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan kwallon tawagar Masar, Mohamed Elneny ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Arsenal zuwa karshen kakar 2024.

Elneny, wanda ke jinya da ba a fayyace ranar da zai koma taka leda ba, shine wanda yafi kowa dadewa a Emirates.

Mai shekara 30 ya buga wa Gunners karawa 155, tun bayan da ya koma Arsenal da taka leda a 2016 daga Basel.

Elneny ya yi wa Arsenal wasan FA Cup zagaye na uku a karawa da Oxford a watan Janairu, wanda ya ci kwallon farko a 3-0 da Gunners ta yi nasara.