Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta koma ta hudu bayan cin Brentford
Manchester United ta koma ta hudu a teburin Premier League, bayan da ta ci Brentford 1-0 a kwantan wasa a Old Trafford ranar Laraba.
Marcus Rashford ne ya ci kwallo na 15 Premier League a kakar nan - na 28 jimilla da ya ci wa United a dukkan fafatawa a bana.
United ta hau kan Tottenham a neman gurbin 'yan hudu don buga Champions League a badi, bayan da kungiyar Old Trafford ta yi rashin nasara 2-0 a gidan Newcastle United a karshen mako.
Karo na biyu kenan da Brentford ta yi rashin nasara a wasa 17 da ta yi, wadda ke neman gurbin shiga gasar zakaraun Turai a badi
United tana da maki 53 iri daya da na Newcastle ta uku, wadda ta caskara West Ham 5-1 a kwantan wasan da suka buga ranar Laraba.
United mai kwantan wasa daya ta bai wa Tottenham tazarar maki uku, wadda ta koma ta biyar a teburin Premier League.
Brentford tana ta tara da tazarar maki shida tsakaninda da Brighton ta shidan teburi.