Arsenal ta bai wa Man City tazarar maki takwas a Premier

An wallafa

Arsenal ta doke Crystal Palace da ci 4-1 a wasan mako na 28 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal ta ci kwallayen ta hannun Gabriel Martinelli da Granit Xhaka da kuma Bukayo Saka da ya zura biyu a raga.

Kenan Saka ya ci kwallo 13 a dukkan karawa a bana a Arsenal har da 12 a Premier League - kakar da ya ci kwallo da yawa kenan.

Ita kuwa Palace ta zare daya ta hannun Jeff Schlupp, bayan da suka koma hutu a zagaye na biyu kenan.

Arsenal ta ci wasa 22 kenan a babbar gasar Premier League ta kakar nan, fiye da wadanda ta ci a bara.

Gunners ta hada maki 69 kenan ta ci gaba da zama ta daya a teburi da tazarar maki takwas tsakaninta da Manchester City ta biyu mai maki 61.

Ta ci wasa shida a jere a bana ta kuma yi bajintar Newcastle Uniteda, wadda ta yi hakan tsakanin Oktoba zuwa Disambar 2022.

Haka kuma karo na biyu kenan da ta yi nasara a wasa a shida a jere a Premier League karkashin Mikel Arteta.

Palace wadda ta buga wasan karkashin kociyan matasanta 'yan shekara 21, Paddy McCarthy, bayan da ta kori Patrick Vieira tana ta 12 a teburi da maki 27.

Tazarar maki uku ne tsakaninta da West Ham ta ukun karshe mai kwantan wasa mai maki 24.

Manchester City mai kwantan wasa daya ta ci Burnley 6-0 ranar Asabar ta kai daf da karshe a FA Cup na bana.

Arsenal wadda rabon ta dauki Premier League tun 2004 karkashin Arsene Wenger, am fitar da ita daga Europa League a hannun Sporting.

Haka kuma City ce ta cire ta a FA Cup, sannan Manchester United ta lashe Carabao Cup na bana.

Saura wasa 10 a kammala kakar bana, ranar Asabar 1 ga watan Afirilu, Gunners za ta karbi bakuncin Leeds United a wasan mako na 29 a gasar Premier League.