Tsananin zafi na iya janyo ɓari ga mata - bincike

Sumathi a gonar Tiruvannamalai
Bayanan hoto, Sumathy mai siyar da gurji ta rasa jariri makonni 12 da ɗaukar cikinta
    • Marubuci, Tulip Mazumdar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global health correspondent
  • An wallafa

Wani sabon bincike daga Indiya ya nuna cewa yin aiki a cikin matsanancin zafi na iya ƙara hatsarin haihuwar jarirai ba rai da kuma ɓari ga mata masu juna biyu.

Binciken ya gano cewa hatsarin da ke tattare da mata masu juna biyu ya fi yadda ake tunani a baya.

Masu bincike sun ce lokacin zafi na iya shafar ba kawai mata a wuraren da ake fama da yanayin zafi ba, har ma a kasashe irin su Burtaniya.

Binciken wanda Cibiyar Nazarin Ilimi da Bincike ta Sri Ramachandra (SRIHER) ta gudanar a Chennai a shekarar 2017, ya shafi mata masu juna biyu 800 daga jihar Tamil Nadu da ke kudancin kasar.

Binciken ya bayyana cewa matan da ke aiki ko sana'o'i a wurare da ke fuskantar matsanancin zafi kamar noma sun fi fuskantar hatsari mafi girma idan aka kwatanta da waɗanda ke aiki a cikin wurare masu sanyi kamar makarantu da asibitoci,

Masu binciken suna so a bai wa mata masu juna biyu a duniya da ke aiki cikin matsanacin zafi taƙamaiman shawarwarin lafiya da za su bi..

Tasirin zafi ya dogara da abin da mutane suka saba da shi, a cewar Farfesa Jane Hirst, daya daga cikin masana kimiyyar binciken.

A cikin manyan filayen Tiruvannamalai, na haɗu da Sumathy. Ta cire safar hannunta masu kauri tana murza yatsun hannunta, wadanda suka kwashe awanni biyu suna girbin gurji ko kokumba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Hannuna na ciwo cikin wannan yanayi na zafi," in ji ta tana murza yatsunta.

Duk da cewa lokacin rani bai fara ba, yanayin zafin na yau ya kai ma'aunin Celsius 30, wanda zafi ya tsananta.

Dole ne Sumathy ta kare hannayenta yayin da take girbe roron kokumba din masu tsauri, amma kuma safar hannun suna haifar da zufa mai yawa.

Ta kara da cewa "Rana tana ƙona min fuska".

Tana zuwa gonar kokumba ɗin ne kafin da kuma bayan babban aikinta, tana aikin dafa abinci a makaranta, kuma ana biyanta kusan rupees 200 ko kuma ƙasa da £2 kawai don ƙoƙarinta.

Sumathy na ɗaya daga cikin waɗanda aka fara dauka a matsayin ma'aikaciya.

Jaririn nata kuma yana daya daga cikin wadanda suka fara mutuwa a binciken.

"Na kasance ina jin gajiya sosai kasancewar ina da ciki kuma ina aiki a cikin zafi," in ji ta.

Wata rana, yayin da Sumathy ke kai wa mijinta abincin rana, sai ta ce ta fara jin rashin lafiya.

Daga baya da maraice, ta ziyarci wani likita wanda ya sanar da ita cewa ta sami ɓarin a cikin makonni 12 na cikin.

"Mijina ya kasance yana rarrashi na sosai a lokacin da na samu ɓari, da baya nan, da ban san yadda zan yi ba."

Wani abin baƙin ciki kuma shi ne mijinta ya rasu kwanan nan, ya bar ta a matsayin mai ba da hidima ga sauran iyalenta.

Duk da irin son da take masa, dole ne Sumathy ta saba da rayuwa ba tare da shi ba.

Yayin da take tunanin mutuwar jaririnta a ciki, Sumathy ba ta da tabbas game da alaƙanta ɓarin cikinta da aiki cikin tsananin zafi ba.

Amma gabaɗaya, binciken ya gano cewa matan da suke yin aiki a yanayi iri ɗaya kamar nata sun fi waɗanda ke aiki a wurare masu sanyi shiga hatsarin haihuwar jariri ba rai ko ɓarin ciki.

Muhimmanci ga mata a duk faɗin duniya

A cewar Farfesa Hirst, likitar mata kuma farfesa a fannin kiwon lafiyar mata na duniya a Cibiyar George, mata masu juna biyu a cikin binciken Indiya suna kan gaba wajen fuskantar sauyin yanayi.

Yayin da ake sa ran matsakaicin zafin duniya zai karu da kusan digiri uku nan da karshen karni idan aka kwatanta da matakan da aka riga aka kafa masana'antu, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin wata mummunar barazana ga bil'adama, musamman ga mata masu juna biyu wadanda ka iya fuskantar mummunan sakamako.

Rekha Shanmugam na auna zafin rana a filayen sukari a cikin Tiruvannamalai
Bayanan hoto, Rekha Shanmugam na auna zafin rana a filayen sukari a cikin Tiruvannamalai

Binciken da aka gudanar a baya a kasashe masu tasowa kamar Amurka da Australia sun nuna karuwar kashi 15 cikin 100 na hatsarin haihuwar bakwaini da haihuwar ɗa ba rai lokacin zafi.

Ko yaya, sabon binciken da aka samu daga Indiya, kamar yadda Farfesa Hirst ta bayyana, sun haifar da damuwa sosai.

Farfesa Hirst ta lura cewa yayin da Burtaniya ba za ta iya fuskantar yanayin zafi kamar Indiya ba, ana iya samun munanan illolin kan masu juna biyu a ƙananan yanayin zafi.

Duk da haka, ta jaddada mahimmancin kiyaye waɗannan hatsari a cikin hangen nesa, saboda fuskantar asarar ciki ko ɓari.

A halin yanzu, babu wata shawara ta duniya ga mata masu juna biyu da ke aiki a yanayin zafi.

Shawarwarin da ke akwai a ƙasa su ne akan binciken da ya shafi maza a cikin sojojin Amurka daga shekarun 1960 da 70s.

Farfesa Hirst tana fatan wannan binciken, tare da ƙarin bincike, zai haifar da samar da ƙa'idojin da suka dace ga mata masu ciki da ke aiki a cikin zafi.

A halin yanzu, ta shawarci mata masu juna biyu da su kare kansu ta hanyar:

  • Gujewa tsawon lokaci a cikin zafi
  • Samun hutawa a cikin inuwa akai-akai idan suna aiki a waje cikin zafi
  • Nisantar motsa jiki ko daɗewa cikin rana.
  • Mata masu ciki su kasance suna shan ruwa ko da yaushe.

Ga binciken da aka yi a Indiya, masu binciken sun yi amfani da ma'aunin abin da ake kira wet-bulb-globe-temperature (WBGT), wanda ke auna tasirin yanayin zafi da saurin iska da kuma hasken zafi a jikin dan adam.

Sakamakon WBGT sau da yawa ya kan yi ƙasa da yanayin zafi da kuke iya gani ana hakawa a TV ko manhaja ta yanayi.

Matsakaicin yanayin zafi ga mutanen da ke yin aiki mai nauyi shi ne digiri 27.5C WBGT, a cewar Hukumar Tsaro da Lafiya ta Amurka.

'Babu wani zaɓi face yin aiki a rana'

A cewar wani bincike na baya-bayan nan daga Jami'ar Cambridge, ana sa ran Indiya za ta kasance cikin kasashe na farko da yanayin zafi ya wuce iyaka ga masu lafiya da ke hutawa a cikin inuwa.

A shekara ta 2050, ana hasashen adadin kwanakin zafi da dare, lokacin da jiki ke fama da farfaɗowa daga zafin rana, zai ninka ko sau huɗu.

A cikin filayen sukari na Tiruvannamalai, Rekha Shanmugam, jagorar binciken SRIHER kuma tsohuwar ma'aikaciyar jinya, tana auna zafin rana.

Ma’aikata da ke kewaye da su, wadanda rabinsu mata ne, ta bayyana cewa da yawa ba su da wani zabi illa yin aiki cikin rana saboda bukatun kudi.

Shanmugam tana duba yanayin zafi, tana nuna cewa yana sama kuma yana iya haifar da haɗarin cututtukan da ke da alaƙa da zafi, musamman game da mata masu juna biyu.

Sandhya
Bayanan hoto, Mata kamar Sandhiya sune ƙashin bayan ma'aikatan Indiya na yau da kullun

Sandhiya, mai shekaru 28, ta ce min ba ta da wani zabi illa ta yi irin wannan aikin mai wahala wanda ake biyanta kusan Rupee 600, kasa da euro shida a rana.

Tana da yara ƙanana guda biyu da sauran dangi da take ciyarwa.

Sandiya kuma ta shiga cikin binciken - kuma ta samu ɓari na farko watanni shida da samun juna biyu.

Sai da ta ɗauki hutun watanni da dama domin ta farfado kuma ta ce har yanzu tana biyan basussukan da ta tara a wancan lokacin.

"Dukkan wata sha'awata sun shafi 'ya'yana ne," Sandiyya ta gaya mani. "Ina son su yi karatu da kyau kuma su sami ayyuka masu kyau, ka da su ƙare da wahala a nan a gonaki kamar ni."

Matsalar fitsari

Ba a fahimci hanyoyin da ke kewaye da yadda da kuma dalilin da ya sa zafi ke shafar mata masu juna biyu da jariran cikinsu ba.

Wani bincike da aka gudanar a ƙasar Gambiya a baya ya nuna cewa yawan zafin jiki na iya tayar da bugun zuciyar da rage gudun jinin jaririn ta hanyar igiyar cibiya.

Wata ka'ida ita ce idan mahaifiyar ta kwashi zafi sosai, ana iya karkatar da jini daga cikin ɗan tayin, don taimakawa uwar hucewa .

Ta ce wani bincike da aka yi a baya ya nuna cewa mata da yawa ba sa son yin fitsari a fili don haka za su guji shan ruwa, suna samun matsalar yoyon fitsari a sakamakon haka.

Neman mafita

An dauki sakamakon binciken a Tamil Nadu da muhimmanci, in ji Dr TS Selbavinayagam, daraktan kula da lafiyar jama'a na jihar.

"Mun riga mun ba da diyya ta kuɗi ga mata masu juna biyu," in ji shi.

Gwamnatin jihar ta bai wa mata matalauta rupees 18,000 idan sun kai makonni 12 na ciki, don kokarin rage musu wasu matsalolin kudi.

Koyaya, yawancin ikon kare waɗannan ma'aikata masu ƙarancin albashi yana kan shugabannin wuraren aiki.

Mr X Bhasker

Asalin hoton, Mr X Bhasker

Bayanan hoto, Thillai Bhasker ya gina rufin karfe don samar da inuwa da ake bukata ga ma'aikatan sa bulo.

A wajen birnin Chennai, Thillai Bhasker - mai ginin tukwane - ya gina katafaren rufin karfe tare da lullubi na musamman na kare zafi, don bai wa ma'aikatansa inuwa da suke buƙata.

"Ya kamata masu kasuwanci su kasance masu wayo don sanin yadda za su rike ma'aikata," in ji shi. "Idan ka kula da su, za su kula da kai."

Ya kuma shaida mana cewa yana shirin gina bandaki na mata kawai.

Wasu kungiyoyi kuma suna ba da tarurrukan ilimi da shawarwari kan matakai masu sauki da mata za su bi don kare kansu a cikin zafi. Ana kuma samar da kwalabe don sanyaya ruwan sha.

Sumathy ba ta da wani zaɓi illa ta ci gaba da aiki cikin matsanancin zafi lokacin da ta sake samun juna biyu cikin shekaru biyu da ɓarin cikinta.

Amma ta samu takamaiman shawarwari daga likitoci da masu binciken SRIHER kan yadda za ta fi kare kanta. Alhamdulillahi ta haifi 'ya mace da namiji lafiya.