Man United za ta kara da Liverpool a Premier wasan hamayya

An wallafa

Manchester United da Liverpool za su fafata a wasan mako na uku a gasar Premier League ranar Litinin a Old Trafford.

Kungiyoyin biyu ne ke kan gaba a taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda tsakaninsu suka lashe kofin lik 39 jumulla.

Sai dai a ranar Litinin idan kungiyoyin sun fuskanci juna, kowacce na fatan cin wasan farko a kakar bana a Premier League.

Liverpool ta yi canjaras biyu da fara kakar nan da yin 2-2 a gidan Fulham, sannan ta tashi 1-1 da Crystal Palace a Anfield a makon jiya.

Jurgen Kloop na fama da 'yan wasan da ke jinya, sannan sabon dan kwallon da ya dauka a bana kan fam miliyan 64, Darwin Nunez ba zai buga karawar ba,

Dan wasan ya karbi jan kati a Anfield a karawa da Palace, kenan ba zai buga wasa uku ba da ya hada da na United da Bournemouth da kuma Newcastle.

United ta sha kashi a wasa biyu a jere karkashin sabon koci Erik ten Hag, bayan da Brighton ta ci 2-1 a Old Trafford, sannan Brentford ta yi nasara da ci 4-0 a makon jiya.

Bayan da United ta yi rashin nasara a wasa biyu a karshen 2021/22 karkashin Ralf Rangnick, kungiyar za ta kaucewa rashin nasara biyar a jere.

Rabon da ta yi wannan rashin bajintar tun daga tsakanin Janairu zuwa Maris din 1972.

Sai dai kuma wasu rahotanni na cewar magoya bayan United za suyi zanga-zanga kafin wasan tsakanin United da Liverpool din, domin nuna bacin rai kan yadda iyalan Glazer ke gudanar da kungiyar.

Ko Liverpool za ta koma kan ganiya a Old Trafford?

United ta kasa cin Liverpool a wasa takwas baya da suka fafata, inda kungiyar Anfield ta hada maki 18 daga 24.

Tun bayan da Liverpool ta caskara United a Maris din 2018, kungiyar ta sallami masu horar da ita biyu wato Jose Mourinho da Ole Gunnar Solskjaer.

Har da kociyan rikon kwarya Michael Carrick da daukar Ralf Rangnick, yanzu ta nada Erik ten Hag, wanda ya fara jan ragamar kungiyar da kafar dama a bana.

Liverpool ta zura kwallo 13 a ragar United a wasa uku baya da suka kara har da cin tara ba tare da ko daya ya shiga ragarta ba.

Bayan da Liverpool ta doke United 5-0 a bara, Solskjaer ya ja ragamar wasa hudu daga baya aka sallame shi.

Dan wasan tawagar Masar, Mohamed Sala ya ci United kwallo shida a wasa uku baya da ya buga, jumulla yana da tara a raga, zai zama na farko a Liverpool da zai ci kungiyar Old Trafford kwallo 10 ko fiye da hakan.

Liverpool na fatan doke United karo hudu a jere a lik a karon farko tun bayan Janairun 2002, tana fatan cin wasa uku a jere a Old Trafford a karon farko.