Arsenal ta ci kwallo mafi yawa a waje a Premier bayan casa West Ham

An wallafa

Arsenal ta zuba ƙwallaye mafi yawa a Premier League a waje a tarihi, bayan da ta caskara West Ham United 6-0 ranar Lahadi.

Karawa ce ta hamayya tsakanin kungiyoyin da ke wasa a birnin Landan a babbar gasar tamaula ta Ingila fafatawar mako na 24.

Wannan nasarar da Gunners ta samu ya sa ta koma ta biyun teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool mai jan ragama.

Tun wasan na ranar Lahadi, Arsenal tana mataki na uku ne, biye da Manchester City ta biyu, wadda ta doke Everton 2-0 ranar Asabar a Etihad.

Wannan shi ne wasan da aka zura kwallaye da yawa a ragar West Ham United a Premier League, bayan wanda Blackburn ta dura mata 8-2 a 1963-64.

Tun kan hutu Gunners ta zura 4-0 a ragar West Ham ta hannun William Saliba da Gabrie da Bukayo Saka da kuma Leandro Trossard.

Bayan da suka huta suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ka kara ƙwallo biyu ta hannu Saka, wanda ya ci biyu a karawar, sannan Declan Rice ya ci na hudu.

Rice dai bai yi murnar cin kwallon da ya yi wa tsohuwar kungiyarsa, sai dai magoya bayan West Ham sun yi ta daga rigar ɗan ƙwallon a filin wasan.

Wannan shi ne wasa na uku da suka kara a tsakaninsu a bana, inda West Ham ta fitar da Gunners da cin 3-1 a League Cup ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba.

Sannan West Ham ta je ta ci Arsenal 2-0 ranar 28 ga watan Disamba a wasan farko a Premier League na kakar nan da suka kece raini a Emirates.