An bai wa Newcastle damar daukar aron 'yan wasa daga gasar Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images
Za a bar Newcastle United ta dinga daukar aron 'yan wasa daga gasar Saudiyya a watan Janairu, bayan da aka kada kuri'a kan batun.
Tun farko kungiyoyin Premier League ne suka ki amincewa da tsarin, abin da ya kai an dakatar da batun na dan wani lokaci.
Masu buga Premier League su 13 ne suka kada kuri'ar kin amince da barin wadda ta mallaki kungiya a gasar ta dauki aron 'yan wasa daga kasarta.
Kenan zaben ya gaba da kuri'a daya, hakan na nufin Newcastle United za ta iya daukar aron 'yan wasa daga babbar gasar tamaula ta Saudiyya.
Hakan na nufin Newcastle United za ta iya daukar aron dan kwallo daga kungiyar da masu zuba hannun jari daga Saudiyya suka mallaka.
An kammala cinikin Newcastle kan fam miliyan 30 a watan Oktoban 2021, wadda ake cewa za ta dauki aron tsohon dan kwallon Wolverhampton, Ruben Neves daga Al-Hilal.
Tun farko an dakatar da bukatar hakan na dan lokaci har zuwa lokacin da za a cimma matsaya kafin a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta nahiyar Turai.
Amincewar na nufin sai dai a dauko aron dan wasa ba wai a bayar da aronsa daga Newcastle zuwa gasar Saudiyya ba.
Masu zuba jari daga Saudiyya suna da kaso 80 cikin 100 a Newcastle, wadda ta mallaki manyan kungiyoyi hudu a Saudiyyar a watan Yuni.
Kungiyoyin sun hada da Al-Nassr da Al-Hilal da Al-Ahli da kuma Al-Ittihad.











