Lokutan da Sarauniya Elizabeth ta kasance cikin raha da barkwanci
Daga Sean Coughlan, wakilin BBC a Fadar Sarauniya

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniya Elizabeth wadda ta shafe shekara 70 kan karagar mulkin Birtaniya, ta jagoranci masarautar ƙasar a lokutan da aka shiga tashin hankali.
Rayuwar da ta rinƙa yi a bainar jama'a a tsare take, inda a kullum fuskarta kan kasance ba yabo ba fallasa ta fuskar raha, amma a 'yan shekarun baya-bayan nan, an rinƙa ganin yadda raha sosai ke bayyana a fuskar basarakiyar.
A wata hira da BBC a farkon wannan shekarar, jikanta Duke na Sussex wato Yarima Harry, ya ce babbar ɗabi'ar kakar tasa ita ce ''raha da barkwanci''
Masanin tarihi kuma mawallafi Sir Anthony Seldon, ya ce kasancewar ba ta dauki rayuwar kashin kanta da muhimmanci ba, ''ya taimaka matuka wajen samun nasarar mulkinta''
''Barkwanci wani abu ne muhimmi ga rayuwa, a cewar Robert Lacey, wani masanin tarihin gidan sarautar.
Ga jerin wasu wasu lokutan da Sarauniyar ta nuna barkwanci da raha a bainar jama'a.
Ganawar shan shayi tare da Paddington Bear

Asalin hoton, Getty Images
A wani ɓangare na bikin cikarta shekara 70 a kan karagar mulki da aka gudanar a watan Yunin wannan shekara a fadarta, an nuna Sarauniyar tana dariya lokacin ganawarta da Paddington Bear, wani mai fitowa a shirin barkwanci na yara, wato katun.
A yayin da ake dab da fara bikin, Paddington ya fito da abincin da ya fi so wato Marmalade, da ya boye cikin hularsa domin bai wa Sarauniyar , inda ya ce mata ''kullum nakan ajiye wani don shirin ko-ta-kwana.''
Sai ta yi dariya a yayin da ta fito da nata marmalade ɗin daga cikin jakarta mai launin baki, tana mai cewa ''ka ga nawa nan.''
Soyayyarta ga wasan naƙasassu

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2016, Sarauniyar ta bayyana a wani bidiyo tare da jikanta Yarima Harry domin ƙarfafa wasannin naƙasassu.
Sarauniyar tare da Yarima Harry sun kalli saƙon bidiyon da shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama tare da matarsa Michelle Obama suka aiko wa ariman, inda suka nuna goyon bayansu ga yadda Yarima Harry ke sha'awar wasannin naƙasassu.
Sarauniyar ta yi dariya lokacin da suke kallon saƙon tana mai cewa ''gaskiya ne wannan.''

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwararriyar mai kwaikwayo
A zarihirance, an ce Saruniyar ƙwararriyar mai kwaikwayo ce, domin kuwa takan yi magana da karin harshe daban-daban kamar yadda Mista Lacey wani masanin tarihi ya bayyana.
An kuma san ta da yin abubuwan burgewa na tsohon shugaban Rasha Boris Yeltsin, kamar yadda mawallafin - littafin Wicked Wit of Queen Elizabeth II - ya bayyana

Asalin hoton, Getty Images
Takan kuma kwaikwayi wasu 'yan siyasa da jaruman talabijin.
Mista Lacey ya bayyana barkwancin a matsayin ''wani abu da yake sanya Sarauniyar farin ciki.''
Yanka kek da takobin sarauta

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniyar ta yanka kek masu tarin yawa a rayuwarta, to amma wasu da yawa da takobin sarauta ta yanka su.
Ta taba yin haka a wani taro da aka gudanar a Cornwall.
A lokacin da wani daga cikin masu shirya bikin ya tunasar da ita cewa ''akwai wukar yanka kek'', sai ta yi murmushi! ta ce ''na sani '' ta ci gaba da jujjuya takobinta'' cikin raha.
Haduwarta da 'yan yawon bude ido
Misis Dolby ta ce tana matukar son labarin haduwar Sarauniya da wasu Amurkawa 'yan yawon bude ido lokacin da suka gamu da ita tare da mai gadinta a kusa da fadarta da ke Balmoral.
Ba tare da sanin cewa ita ba ce, sai 'yan yawon bude idon suka tambaye ta cewa ''Kin taba ganin Sarauniya kuwa?''
Sai ta yi murmushi ta ce ''A'a, sai dai ku tambayi wancan'' ta nuna mai gadinta.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma a wani kantin sayayya da ke Norfolk, lokacin da yaron shagon ya kalle ta, sai ya ce mata ''Gaskiya kina kama da Sarauniya.''
Sai nan ma ta yi dariya ta ce ''Yaya aka yi ka san haka, ko ka taɓa ganin Sarauniyar ne?''
Wane ne ke burge Sarauniyar?
Takan yi amfani da barkwanci wajen lallashin iyalanta idan suna cikin damuwa ko fushi.
Sir Anthony ya ce ''Ta san yadda za ta yi domin kawo farin ciki a zukatan mutane ta hanyar yin abubuwan ban dariya.''
Sarauniyar ta hadu da manyan 'yan barkwanci da dama kamar su Tommy Cooper, wanda Misis Dolby ta ce ya taɓa tambayarta cewa ko tana sha'awar wasan kwallon kafa.
Lokacin da ta amsa masa da cewa ba ta da sha'awa, sai ya ce da ita ''To in kawo miki tikitin kallon wasan karshe na FA?''

Asalin hoton, Getty Images
An ce fitaccen mai wasan barkwanci na gidan talabijin din British TV, Kumar, shi ne mutumin da ya fi burge Sarauniyar.
Sanyaya zuƙatan al'umma
Sarauniyar kan yi amfani da wuraren taruka domin kwantar wa al'ummar kasar hankali a lokacin da kasar ke cikin halin damuwa.
Audrey Tang ta Ƙungiyar Masana Halayyar ɗan-Adam ta Birtaniya ta ce dariya wani muhimmmin makami ne da ake amfani da shi wajen sanyaya zukata idan suna cikin damuwa.
"Wannan alama ce ta lallashin zukata.''

Asalin hoton, Getty Images
Dariya tana taimaka wa lafiyar mutane tare da rage damuwa.
Yin dariya abu ne mai kyau, to amma ba a kowanne lokaci ba ne ya dace da dariyar.
Dakta Tang ya ce akwai wasu abubuwa na halitta da kan sanya mutane dariya saboda halin da suke ciki, ko kuma don suna son lallashin zukatan masu fushi.

Asalin hoton, Getty Images
Chris Young wani mai ɗaukar hoto ya ɗauki hoton Sarauniyar tana dariya a lokacin da gungun ƙudan zuma ya tarwatsa taron sake fasalin soji da aka shirya a fadarta da ke Windsor a shekarar 2003.
Mista Young ya ce ''Ta riƙa dariya kamar ƙaramar yarinya.''
A wani saƙon bikin Kirsimeti da ta aike wa al'ummar kasar a shekarar 1991, Sarauniyar ta nuna tsantsar barkwanci a cikin sakon.
''Kar mu ɗora wa kanmu girman kai'', kamar yadda ta ce a saƙon.
''Kowa na da hikimar da Allah Ya hore masa.''












