Damben Autan dan Bunza da Ilele

Damben gargajiya
An wallafa
Bayanan bidiyo, Damben Ilele da Autan dan Bunza ajon Dan Ali

Ranar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya ya karrama Dan Alin ba ta isarka a damben safe.

Kudawa da yawa sun halarci damben don ganin sun fitar da Dan Ali kunya, inda aka yi dambe da dama.

Ga jerin wasannin da aka fafata:

To bari mu fara da damben manya da aka yi tsakanin Shagon Autan dan Bunza daga Jamus da Ilele shagon Garkuwan mai caji daga Kudu.

Damben ya kayatar a turmi biyu da suka yi, sai dai ba kisa.

Yalo Dan Zuru Guramada ya dambata da Abba Dogon Sisco daga Kudu, inda suka yi turmi uku ba kisa aka raba su.

Shi kuwa Koronabirus Shagon dan Alin bata isarka daga Kudu mai biki, wasa biyu ya buga, inda ya fara doke Dogon mai masaukin baki Guramada, ya kuma yi turmi daya da Shagon Tanko na Tunga shima Guramada amma ba kisa.

Damben Aljanin Arewa da Biyun Sama’ila daga Kudu tumi uku suka yi, ba a fidda gwani ba.

Dan Dabar Autan dan Bunza daga Arewa ya doke Shagon mai masauki Guramada, Bahagon Yalo dan Zuru gudamada ya yi nasara a kann Dogon Shagon Gwagwarwa daga Kudu.

Sai wasan da Garkuwan Autan dan Bunza daga Arewa ya buge Shagon Champion daga Kudu a dan kankanin lokaci.