Sevilla ta amince za ta dauki Isco tsohon dan wasan Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Sevilla ta sanar cewar ta cimma yarjejeniya za ta dauki Isco, tsohon dan kwallon Real Madrid, wanda bai da kwantiragi a yanzu haka.
Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 30 ta kare a watan Yuni, bayan kaka tara da ya yi a Santiago Bernabeu, wanda bai samu buga wasanni ba sosai karkarkashin Carlo Ancelotti.
Isco ya bar Real Madrid bayan lashe kofuna da yawa a kungiyar ciki har da La Liga uku da Champions League biyar.
Dan kwallon ya buga wa tawagar Sifaniya wasa 38, sai dai rabon da ta gayyace shi tun bayan 2019,
Idan Isco ya kammala komawa Sevilla zai sake taka leda karkashin Julen Lopetegui wanda ya horar da Sifaniya da kuma Real Madrid.
Sevilla ta tabbatar cewar ranar Litinin za ta auna koshin lafiyar Isco daga nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu a kungiyar.
Kungiyar Sevilla za ta fara kakar bana ta 2022/23 a gasar La Liga da Osasuna ranar Juma'a.









