Tottenham ta dauki mai tsaron bayan Middlesbrough Spence

Asalin hoton, Rex Features
An wallafa
Tottenham ta kammala daukar mai tsaron bayan Middlesbrough, Djed Spence kan yarjejeniyar kaka biyar.
Mai shekara 21, mai tsaron baya daga gefen hagu ya buga wasannin aro a kakar da ta wuce a Nottingham Forest, wadda ta samu gubin buga Premier League a karon farko tun bayan shekara 23 rabon ta da gasar.
Ya yi wa Forest wasa 42 a Championship da cin kwallo biyu da bayar da hudu aka zura a raga.
Spence, wanda ya buga wa tawagar Ingila ta matsa 'yan kasa 21, ya je Middlesbrough a 2018 daga matasan kungiyar Fulham.







