Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Rasha ke murna da juyin mulkin Burkina Faso
A juyin mulkin baya-bayan nan da aka gudanar a kasar Burkina Faso an ga wasu matasa rike da tutar kasar Rasha a wata zanga-zangar nuna goyon baya ga juyin mulkin da aka gudanar a Ouagadougou babban birnin kasar, wani abu da zai kara dadada wa kasar Rasha wacce ke kokarin samun goyon bayan kasashen yankin Nahiyar Afirka
Duk da cewa ba su da yawa, to amma hakan ya haddasa rade-radin zargin hannun Rasha a juyin mulkin da Kaftin IbrahimTraore ya kwace Mulki a kasar wacce ke fama da tashe-tashen hankula masu alaka da masu ikirarin jihadi.
Yevgeny Prigozhin, wani kusa da ke da kusanci da shugaban Rasha Vladimir Putin, kuma jagoran sojojin hayar Rasha da ake kira ‘Wagner’ wadanda ke ayyukansu a wasu kasashen Afirka , ya taya sabon shugaban mulkin sojin Burkina Faso murna, yana mai bayyana shi a matsayin’’halastaccen da mai cike da soyayya da kishin kasarsa’’
Ya kara da cewa ‘’Al’umar Burkina Faso sun kasance a karkashi akalar Turawan mulkin mallaka, wadanda suka lalata kasar, tare da yin wasa da hankulan al’umar kasar, ta hanyar horar da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji wadanda ke tayar da zaune tsaye a kasar’’.
Anan yana hanunka-mai sanda ne ga Faransa, wacce ta yi wa kasar mulkin mallaka.
Bayan daga tutar kasar Rasha da masu goyon bayan juyin mulkin suka yi, har hari suka kai kan gine-ginen Faransa ciki har da ofishin jakadancinta a Burkina Faso.
Wannan zanga-zangar ta aika sako tare da karfafa gwiwwa ga sauran wadanda ke adawa da Faransa a nahiyar Afirka.
Kasar Faransa dai ta kwashe kusan shekara 10, tana kokarin taimaka wa sojojin yankin Sahel wadanda suka hada da Burkina Faso wajen yakar ayyukan masu ikirarin jihadi, wadanda wasunsu ke da alaka da kungiyoyin Alka’ida da ISIS.
To amma a baya-bayan nan ta fice daga makwabciyar kasar Mali, bayan samun sabani da shugabannin mulkin sojin kasar, wadanda ake zargi da mayar da hankali wajen neman taimako daga kasar Rasha domin yakar ‘yan ta’adda.
An Ambato Sergei Markov ministan harkokin wajen Rasha na cewa ‘’dakarunmu za su taimaki sabon shugaban kasar’’.
Jim kadan bayan ya karbi mulki Kaftin Traoré ya bayyana karara cewa yana bukatar yin aiki tare da sabbin kawayen kasashe domin fatattakar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi wadanda ke damun kasar tun shekarar 2015.
Inda wasu da dama suka ce Rasha yake nufi da ‘sabbin kawaye’
To amma game da manufarsa ta fatattakar masu ikirarin jihadi, ya ce zai yi aiki da Amurka da duk wata kasa da ke son taimaka wa zaman lafiyar kasarsa.
Amurka na jagorantar horar da dakarun yankin yammacin Afirka game da yaki da ‘yan ta’adda, da take shiryawa shekara-shekara, to sai dai wannan shekarar Burkina Faso da Mali basu halarta ba.
Dr Raman na cibiyar nazarin dakarun Amurka ya ce ‘’ya kamata Burkina Faso ta kauce wa tarkon da Mali ta fada’’.
Yana mai cewa gwamnatin mulkin sojin Mali na biyayya ga kasashen Turai da Amurka tun lokacin da ta kwace Mulki a shekarar 2020.
‘’Yanzu kacokan kasar ta dogara da kasar Rasha, in kuwa suka sake Rasha ta shigo kasarsu to ba za ta taba fita cikin sauki ba, abin da ya faru kenan ga kasar jamhuriyar Afirka ta tsakiya’’.
Kungiyar Wagner ta kasar Rasha dai na gudanar da ayyukanta a jamhuriyar tsakiyar Afirka tun shekarar 2018, ana kuma zargin dakarunta da keta hakkokin bil-adama, wadanda suka hadar da kisan kiyashi, da azabtarwa, da batar da mutane da fyade.
Dakta Sorcha MacLeod na jami’ar Copenhagen kuma jagoran sojojin haya na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ‘’kungiyoyi irinsu Wagner koma-baya ne ga ci-gaban zaman lafiyar kasa’’ .
Amurka ta yi zargin cewa ‘’Sojojin hayar Rasha na kwasar albarkatun kasashen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Mali da Sudan domin samar da kudin da take yakin Ukraine da su.
A wani kakkausan sako da ya fitar a makon da ya gabata, jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ya ce wannan batu na ci wa kasashe Afirka tuwo a kwarya.
Duk da cewa dakarun sojojin hayar Rasha sun fara aiki a kasar Mali kasa da shekara guda, alamun farko na nuna cewa ayyukan mayakan jihadi na ci gaba da karuwa, tare kuma zarge-zargen take hakkin bil-adama.
Kasar Mali na ci gaba da kasancewa sansanin mayakan yankin sahel, wadda ke fuskantar yawan hare-hare cikin wannan shekara.ReplyForward