An tuhumi Van Dijk saboda jan katin da aka yi masa a Newcastle

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhmi Virgil van Dijk a kan jan katin da aka ba shi a wasan da Liverpool ta doke Newcastle United a Premier League.

An bai wa kyaftin din Liverpool jan kati kai tsaye a minti na 29 a St James Park ranar Lahadi, saboda ƙetar da ya yi wa Alexander Isak.

Ɗan bayan na ƙasar Netherlands, an nuna shi yana cacar baki da alkalin wasa John Brooks a lokacin da ake duba lamarin a VAR.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila na tuhumar Van Dijk da ''kalaman ɓatanci da na cin zarafi''.

Mai shekara 32 ya kuma yi cacar baki da alkalin wasa mai jiran kar-ta-kwana a lokacin da zai bar filin wasa.

An bai wa ɗan wasan na Liverpool nan da zuwa ranar Juma'a, domin ya kare kansa.

Kawo yanzu, Van Dijk ba zai buga wasa daya ba, saboda jan katin da aka ba shi, kenan ba zai yi karawar da Liverpool za ta buga da Aston Villa ranar Lahadi ba.

Liverpool ce ta yi nasara a karawar da ci 2-1 a wasan mako na uku.