Dan wasan Manchester United Rasmus Hojlund zai yi jinyar mako biyu ko uku

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaban Manchester United Rasmus Hojlund zai yi jinya ta tsawon makonni biyu ko uku sakamakon raunin da ya ji.
Dan wasan da aka saya kan kuɗi fan miliyan 72 ya ci kwallo a wasa shida a jere a gasar Premeir a wasan ranar Lahadi da suka ci Luton 2-1.
Dan wasan Denmark ɗin mai shekara 21 ba zai buga wasan da United za ta yi ba a gida da Fulham a ranar Asabar da kuma zagaye na biyar na gasar FA da za ta yi da Nottingham Forest a ranar Laraba.
Nan da makonni biyu kuma ƙungiyar ta Erik ten Hag za ta buga wasan hamayya sannan kuma ta karbi baƙuncin Everton.
"Ba wani ciwo ba ne na a zo a gani, mako biyu ko uku zai dawo. To haɗari ne a ci gaba da shi a irin atisayen da muke yi," kamar inda Ten Hag ya faɗa a ranar Juma'a.
"Ba wani katon ciwo ba ne, amma dole ya jira."
Hojlund ya ci kwallo 13 cikin wasa 30 da ya buga wa United a duka gasa, tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Atlanta da ke Serie A kan kwantaragin shekara biyar.
Ya kasa zura ko kwallo guda a wasanni 14 na farko a Premier amma tun daga nan yake kokari inda ya zuwa kwallo bakwai ya kuma taimaka aka ci biyu a wasanni shida da suka gabata.
Daya dan wasan gaban da United ke da shi, shi ne Anthony Martial, shi kuma tiyatar da aka yi ma shi ta sa ko wasa baya bugawa.
Scott McTominay shi ne na biyu a yawan cin kwallo a wannan kakar a duka gasa, bayan Hojlund da yake da takwas.












