Rauni ya jefa Liverpool a tsaka-mai-wuya

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool na fuskantar mummunan yanayi sakamakon raunuka da ƴan wasanta ke fama da su yayin da take shirin karɓar baƙuncin Southampton a zagaye na biyar a gasar FA Cup, in ji koci Jurgen Klopp.

Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Holland Ryan Gravenberch, wanda ya samu rauni a idon tsawu, shi ne ɗan wasa na baya-bayan nan da ya shiga jerin ƴan wasan Klopp da ke fama da rauni.

Mohamed Salah da Darwin Nunez da kuma Dominik Szoboszlai sun fara atisaye, amma har yanzu ana shakkun ko za su samu buga karawa da Southampton a Anfield ranar Laraba ba.

An fitar da Gravenberch a kan gadon ɗaukan marasa lafiya yayin wasan ƙarshe na cin kofin EFL da Liverpool ta kara da Chelsea ranar Lahadi.

Ɗan kasar Holland ɗin mai shekaru 21 yanzu ya haɗe da Alisson, da Trent Alexander-Arnold da Joel Matip da Thiago Alcantara da Curtis Jones da Stefan Bajcetic da kuma Diogo Jota a jerin masu jinya.

Klopp ya ce zai jira ya ga yadda Salah, da ɗan wasan gaba Nunez da kuma ɗan wasan tsakiya Szoboszlai za su yi atisaye kafin yanke shawara kan ko za su buga wasan.

Liverpool ta lashe kofinta na farko a kakar wasa ta bana bayan da ta doke Chelsea a Wembley kuma tana da burin ci gaba da farautar dukkan manyan gasanni huɗu da take ciki.