'Akwai yiwuwar Isra'ila ta aikata laifukan yaƙi a Gaza ta hanyar amfani da yunwa'

Yarinya
An wallafa

Bayan shafe makonni ana gargadi, a baya-bayannan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ya fitar da kididdigar da ta nuna yadda bala'in da ake ciki a Gaza ya zama makamin da ake amfani da shi wajen haifar da yunwa.

MDD ta ƙara matsa lamba a kan Isra'ila domin ta yi abubuwan da suka kamata wajen kare Falasdinawa fararen hula, da kuma barin kai kayan agajin da ake bukata ga mutanen da ke bukatarsu.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, wani babban jami'i a hukumar kare hakkin dan'adam ta MDD, Volker Turk, ya ce ana dora wa Isra'ila laifin matsalar yunwar da ake fama da ita a Gaza, saboda tana amfani da yunwa a matsayin makamin da take amfani da shi a yakin na Gaza.

Mr Turk, ya ce idan har aka tabbatar da abin da ake zargi a kan Isra'ilar, to za a iya cewa ta aikata laifin yaki.

Ministan kula da harkokin tattalin arzikin Isra'ila, Nir Barkat, ya hakikance cewa Isra'ilan na bari ana shigar da dukkan kayan agajin da Amurka da ma sauran kasashen duniya suka bukata.

Ya ce MDD ta gaza wajen raba abubuwan da ya kamata idan Hamas ta bayar da dama.

Duk da wannan ikirari na Isra'ila, akwai wasu jerin manyan motoci cike da kayan agajin da ake bukata a zirin Gaza, amma sun maƙale a iyakar Masar da Rafah saboda ba za su iya shiga ba har sai isra'ila ta bayar da dama.

Rashin shigar da kayan da suka kamata ya tursasa wa Jordan da wasu kasashe ciki har da Amurka da Birtaniya jefa kayan agaji ta sama, wadda suke gani ita ce hanya mafi sauki da za a iya kai kayan agaji.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A bangaren su Falasdinawan da ke kasa, wasu na mutuwa sakamakon kokarin ganin sun samu kasonsu a yayin da kayan agajin ke fadawa ruwa ko kuma su danne mutane.

Sojojin ruwan Amurka na tura injiniyoyinsu a wasu wurare domin su rinka taimaka wa wajen fara kai kayan agajin ta ruwa.

Sai dai duk da haka dukkan wadannan hanyoyin ba lallai ba ne su dore har sai Isra'la ta bude titunan da za a iya kai wa Gaza.

Cikin wata hira da aka yi da shi daga Geneva, Mr Turk ya ce akwai shaidun da ke nuna cewa Isra'ila na rike kayayyakin agajin da ake kai wa mutanen Gaza.

Mr Turk ya yi Allah-wadai da hare-haren da Hamas ta kai wa fararen hular Isra'ila da kuma sojoji a ranar 7 ga watan Oktoba, ciki har da kisa da fyade da kuma garkuwa da mutane.

Amma duk da haka ya ce bai kamata wani bangare cikin wadanda ke yakin ya rinka yin wasu abubuwa da ba su kamata ba, ciki har da yunkurin kwace ko rike duk wasu kayan agajin da mutanen Gaza ke bukata ba.

"Dukkan abokan aikina a bangaren agaji na shaida mana cewa abubuwan da ke faruwa ba su dace ba, akwai matsaloli, akwai tarnaƙi...kuma Isra'ila za a dora wa laifi" in ji shi.

"Zan iya cewa a gaskiya akwai bukatar a magance wannan matsala ta rashin isar kayan agaji Gaza."

Idan aka duba batun bala'in da ake ciki a zirin Gaza na rashin kayan agaji ta hanyar kiyasta mutanen da ke cikin azabar yunwa, hakan ya janyo an gargadi Isra'ila da kawayenta a kan su sauya yadda suke yaki a Gaza, su kyale fararen hula, su daina kashe su da kuma barin su da yunwa.

A baya-bayannan an gudanar da bincike wanda hadakar kungiyoyin agaji suka yi, kuma anan ne aka kwatanta irin halin yunwar da ake fama da ita a zirin Gaza, saboda an kiyasta cewa akwai mutum miliyan daya da dubu dari daya - wato rabin al'ummar Gaza ke nan - da ke fama da matsanancin karancin abinci.

Kuma a cikin rahoton binciken an yi bayanin yadda yunwa bala'in yunwar zai iya tsananta nan da makonni takwas da kuma abin da rashin tsagaita wuta zai iya janyo wa a zirin Gaza.

Iyaye Falasdinawan da suke kokarin kai 'ya'yansu marassa lafiya ko wadanda ke fama da yunwa asibitin da ke aiki a Gaza ba sa jiran sai an kirga da su. Sun shafe makonni suna fadi tashi ciyar da su, kuma a kan idanunsu suna gani 'ya'yansu ke mutuwa.

Wata yarinya da ke kwance a asibiti da wani dan jaridar Falasɗinu da ke yi wa BBC rahotanni ya ci karo da ita, ya gan ta kwance a gadon asibiti ba ta magana, ma'ana a halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Yarinyar mai suna Noora Mohammed na fama da lalurar ciwon huhu da hanta, lalurar da ake gani babbace ko da kuwa a lokacin da ake zaman lafiya.

A cikin watannin da aka shafe ana yaki da rashin kayayyakin kula da marassa lafiya, rashin lafiyarta sai tsananta take yi.

Mahaifiyarta ta ce: "'Yata ba ta iya ko motsi, tana fama da karancin jini, a kodayaushe tana cikin bacci, ga shi kuma babu wani abu na gina jiki da take samu."

Ko ba komai an kai Noora asibiti, damar da wasu dubban 'yan kasar suka kasa samu.

Shaidar da ake da ita a kan bala'in rashin kayan agajin da ake fama da shi a Gaza abin tashin hankali ne.

Wasu hotunan asibitin da aka dauka sun nuna yadda gabobin yaran da ke kwance a asibitin suka kumbura, ga rama, duk fatar jikinsu ta yamushe saboda rashin abinci.

Yarinya

Isra'ila ta yi watsi da bukatar kwamitin tsaro na MDD na gaggauta tsagaita wuta.

Nir Barkat, ministan kula da tattalin arzikin Isra'ila, ya ce babu wani abu da Isra'ila za ta samu a yakin nan, bukatarta ta kawar da 'yan Hamas da kuma sako mata wadanda aka yi garkuwa da su.

Kasashen duniyar da ke goyon bayan Isra'ila kamar Amurka su kansu ba su jin dadin yadda Isra'ila ke yakin.

Mr Barkat, ya ce,: "Duk da muna duba yiwuwar kawo karshen yakin nan, za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun kashe 'yan ta'addan Hamas."

"Za mu iya cewa muna yaki ne da mutane marassa imani, muna tsammani kasashen duniya za su goya mana baya har sai mun ga karshensu." in ji shi.

Tuni dai shugaban hukumar kare hakkin dan'adam ta MDD ya soki kalaman Isra'ilan.

"Abu guda da zance shi ne, dole a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawo karshen bala'in yunwar da ake fuskanta a Gaza," in ji shi.