Yadda anobar da ta faru shekaru 700 da suka wuce ke shafar lafiyarku

Asalin hoton, MUSEUM OF LONDON
Irin ɓarnar da annobar ta haifar ya yi mummunar tabo ga kakannin-kakanninmu ta yadda lamarin ke shafar lafiyarmu shekaru 700 bayan faruwar ta.
Kimanin rabin al’umma ne suka mutu lokacin da annobar da aka yi wa laƙabi da ‘Baƙar mutuwa’ ko ‘Black Death’ ta addabi ƙasashen Turai a shekarun 1300.
Wani bincike a kan sinadarin ƙwayoyin halittun gado daga ƙwarangwal ɗin mutanen da suka tsira daga annobar, wanda shi ne bincike irin sa na farko, ya nuna yadda sauyi a ƙwayoyin halitta suka taimaka wa mutane suka tsira daga annobar.
To amma waɗannan sauye-sauye na ƙwayoyin halitta ne kuma ake alaƙantawa da cutuka masu illa ga garkuwar jiki da ake fama da su a yanzu.
‘Black Death’ na daga cikin annoba mafi muni da aka taɓa fuskanta a tarihin ɗan’adam. Inda aka yi iyasin cewa ta hallaka mutum miliyan 200.
Masu bincike sun yi zargin cewar dole ne irin wannan mummunan lamari ya sauya yanayin halittar ɗan’adam.
Sun yi nazari kan ƙwayar halittar gado da ciro daga haƙoran ƙwarangwal ɗin gwarwakin mutanen da suka mutu tun tale-tale, waɗanda aka gano cewar sun rayu ne gabanin mummunar annobar, ko a lokacinta ko kuma bayan annobar.
Ƙasusuwan da aka yi amfani da su wurin nazarin sun haɗa da waɗanda aka ciro daga wasu manyan ƙaburbura a London, sai kuma waɗanda aka samo daga Denmark.

Asalin hoton, MCMASTER UNIVERSITY
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sakamakon da aka samu, wanda aka wallafa a mujallar ‘Nature’ ya mayar da hankali ne kan wani sinadarin ƙwayar halittar gado da ake kira ERAP2.
Idan mutum ya samu sauyi daidai yadda ya kamata, to akwai yiwuwar zai iya tsallake annobar da kimanin kashi 40%.
“Wannan sauyi yana da yawa, yana da yawa sosai, abin mamaki ne a ce an samu irin wannan a cikin ƙwayar halittar gado ta ɗan’adam.” In ji farfesa Luis Barreiro na jami’ar Chicago.
Saboda haka waɗanda suka ci sa’a sun gaji irin wannan sinadarin halittar gado da ya sauya daga mahaifansa biyu.
Daga nan sai ƴaƴan waɗanda suka tsira daga annobar suka gaji irin wannan sinadari na gado daga iyayensu, daga nan sai mutanen da suka gaji irin wannan ƙwayar halittar gado suka yawaita.
Farfesa Hendrik Poinar, masanin sauyin ƙwayoyin halittar gado na jami’r McMaster ya ce “babban lamari ne, an samu sauyi da kimanin kashi 10% a tsawon zamani uku.”
Bayanan da aka samu daga jinin mutanen da suka da irin wannan ƙwayar halittar gado da ta sauya ya nuna cewa sun fi jure wa annoba fiye da waɗanda ba su da ƙwayar halittar da ta sauya.
A yanzu, irin wannan sauyi da ake samu a ƙwayar halittar gado ya yawaita fiye da yadda aka samu jim kaɗan bayan annobar ‘Black Death’.

Asalin hoton, UNIVERSITY OF CHICAGO
To amma matsalar ita ce ana alaƙanta sauyin da cutuka masu illa ga garkuwar jikin ɗan’adam, kamar cutar kumburin ƴaƴan hanji da a turance ake kira ‘Crohn’s’.
Hakan na nufin lamarin da ya kasance taimako ga kakannin-kakanninka shekaru 700 da suka gabata, yanzu ya zamo illa gare ka.
Farfesa Barreiro ya ce garkuwar kashi 40% da aka gano sanadiyyar sauyin da aka samu a ƙwayar halittar gado shi ne mafi ƙarfi da aka taɓa samu tsakanin bil’adama.
Ya zarta irin turjiyar da ake samu tsakanin mutanen da jikinsu ke bijire wa cutar HIV.











