Me ya sa masu karɓar haraji a Najeriya ke amfani da zalama?

Mista Nwokuha ya yi iƙirarin cewa " bayan ansar haraji, yana taka rawa wajen sauƙaƙa zirga-zairgar ababen hawa
An wallafa

Wasu masu kudi a birnin Fatakwal ne da ke gabashin Najeriya suka dauki Mista Nwokuha aikin tattara kuɗaɗan haraji, yana riƙe sanda da ke tsorata mutane a tituna masu cunkuson ababen hawa.

Aikin mutumin ɗan shekaru 34 shi ne ya karɓi haraji daga masu tasi da masu manyan motoci da suke aiki a cikin birnin Fatakwal ɗin.

Sana'ar karɓar haraji tsohuwar al'ada ce, a wancan lokacin masu sana'o'i kan bayar da kyautar kudi ko abun sha, domin kyautata alaƙa tsakanin su da manyan gari.

Sai dai yanzu lamarin ya sauya zani, inda masu suka ke bayyana hakan da wani salo na ƙwace.

Wasu daga cikin masu kuɗin na da'awar cewa suna amsar harajin ne a madadin sauran al'ummar gari, suna karɓar haraji daga ƴan kasuwa da kuma masu tasi da suke aiki a yankin da suke ganin yana ƙarƙashin ikonsu.

Mista Nwokuha ya ce "yana tara naira 5,000 zuwa 7,000 duk rana, kudi masu kauri a Najeriya.

Yana da mata da yara biyu, kuma bayan ya ɗauki kasonsa yana raba wa wasu masu karfin faɗa a ji su biyar a yankinsu, duka kuɗaɗen dai kan zurare a tsakaninsu.

Gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi a Najeriya kan yi amfani da ire-iren waɗannan mutanen wajen ƙarbar haraji.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Mutanen na amfani da asusun bankunan su kuma suna cire wani adadi na kuɗin kafin su saka a lalitar gwamnati," a cewar wani tsohon jami'in tattara haraji Michael Ango.

Gwamnatin tarayya a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu ta ƙaddamar da hanyoyin tattara haraji nata na kanta.

Mista Nwokuha ya yi amannar cewa yana taka muhimmiyar rawa, saboda yana taimakawa wajen sauƙaƙa cunkuson ababen hawa duk da ta haka ne yake saurin damƙe masu tasi.

"Ina sulhunta direbobin tasi idan an samu rikici tsakanin su" inji Mista Nwokuha, wanda ke kai gwaro ya kai mari wajen tattara haraji a ranakun litinin zuwa juma'a.

Kafin direba ya tafi zai biya kashi 20 na kuɗin motar fasinjojin da ya ɗauka.

"Ba'a bayar da dama tasi su dauƙi fasinjoji a nan ba." inji Mista Nwokuha yayin da yake nuna wata alama da ke gefen titi ɗauke da rubutu kalar na ƴan sanda da ke nuni da ba'a tsayawa a wajen.

"Amma idan sun matsa sai sun tsaya a nan to dole su biya kuɗaɗe ga al'umar yankin," kamar yadda ya shaida wa BBC.

A wasu lokuta idan har direba ya ƙi biya za su iya fasa masa madubin gefen direba ko su cire lambar motarsa.

Idan suka yi yunƙurin nuna turjiya kuwa, sai dai su ji bugu a gadon bayansu da sandar da ke hannun Mista Nwokuha.

Wani mai karɓar haraji a Abuja kenan yake cire lambar wata mota domin hana direban tserewa.

Mista Nwokuha yana aikin da ya kamata ma'aikatan ƙananan hukumomi su yi. Najeriya na da yawan ƙananan hukumomi 774 sai dai mafi akasarin su ba su aikin su yadda ya kamata.

Kowa zai iya yin irin abunda Mista Nwokuha ke yi, madamar zai iya tare motoci a hanya tare da ƙaƙaba matakan da suka yi mashi.

Suna tsayawa a bisa tituna da sanda a hannunsu, ko kuma su ajiye duram-duram a kan tituna, da karafuna masu tsini saboda direbobin da ke ƙoƙarin tserewa.

Masu karɓar haraji sun fi yawa a kudancin Najeriya, inda suke tsare manyan hanyoyi a madadin wasu gwamnatocin jahohi.

Wani direban babbar mota ya shaida wa BBC cewa yana biyan naira 80,000 kwatankwacin dalar Amurka 100, a duk lokacin da zai je jihar Imo daga Lagos watau tafiyar tsawon kilomita 540.

"A kwai shingen masu tattara haraji guda 15 tsakanin jihar Edo da Fatakwal watau tafiyar kilomita 280," inji direban babbar motar.

Shi ma da yake karin bayani, wani direba ya ce " harajin kashi-kashi ne, akwai harajin da ake kira da na sauraren rediyo da kuma kuɗin ɗaukar fasinjoji da na sauke su."

Ya ce "banda kuɗaɗen da muke badawa na cin hanci ga jami'an tsaro a duk lokacin da muke tafiya a faɗin ƙasar.

Wani jami'a a cibiyar tattara haraji ta Najeriya, Clement Akanibo, ya bayyyana salon na tattara harajin da fashi da makami.

"Yana haifar da wahalhalu wajen yin kasuwanci yana kuma kara kuɗin da mutum zai kashe a kasuwancinsa," inji shi.

Gwamnatin Tinubu na son ƙananan ƴan kasuwa su yi amfani da  ta hanyar biyan haraji ta zamani

Asalin hoton, Getty Images

Babu wasu bayanai na tsare-tsaren kawo ƙarshen hakan daga gwamnatin Tinubu, amman tabbas yana buƙatar haɗin kan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi saboda aiki ne da ya shafe su.

Gwamnatin Tinubu ta ce tana son inganta hanyoyin karɓar haraji domin kara samun kuɗaɗen shiga saboda ta kara adadin kuɗaɗen da za ta kashe a ɓangarorin lafiya da ilimi, tare da rage basussukan da suka dabaibaye ƙasar.

Gwamnatin Tinubu ta yanke wa kanta hukuncin cewa za ta bunƙasa kuɗaɗen harajin da take karba a cikin shekaru uku masu zuwa.

A yanzu dai gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wajen karɓar haraji, amma ba ta amfani da masu tare hanya don karɓar haraji, sai dai tana tsammanin ƴan kasuwa su biya kai tsaye zuwa ga asusun gwamnati.

A yunƙurin ta na kawo karshen karkatar da kuɗaɗen haraji, gwamnatin na son ta tabbatar da amfani da hanyar zamani wajen biyan kuɗin, inda ta fara haɗa kai da ƙungiyoyin ƴan kasuwa miliyan 40 masu ƙarfin faɗa a ji.

Hakan ba abu ne mai sauki ba, saboda yawancin ƴan kasuwar ba su ajiye bayanan kasuwancinsu kuma ba su taɓa biyan kuɗin haraji ba, ga kuma matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta.

Sai dai, idan har tsare-tsaren suka yi nasara, gwamnatin Tinubu za ta tilasta gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi daina amfani da hanyoyin al'adar da suka saba amfani ta su, kuma ƴan Najeriya za su yi murna da hakan saboda za su tsira daga azabtarwar masu ƙwace ire-iren su Mista Nwokuha.