Nau'ukan kwaɗi da macizan da suka haddasa asarar dala biliyan 16 a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwararru a harkar kimiyya da ke tattara asarar da wasu mugayen ƙwari suka haifar a faɗin duniya sun gano wasu halittu biyu da suka jawo asarar fiye da sauran.
Nau'in kwaɗo ɗan Amurka da ake kira American bullfrog a Turance da kuma jan maciji - da ake kira brown tree snake a Turance - sun haddasa asarar kuɗin da suka kai dala biliyan 16 da 300,000 - kwatankwacin naira tiriliyan shida - faɗin duniya tun daga shekarar 1986.
Ƙari a kan albarkatun tsirrai da suka lalata, mugayen dabbobin sun kuma lalata amfanin gona sannan suka haifar da katsewar wutar lantarki.
Masu bincike na fatan abin da suka gano zai taimaka wajen tara kuɗaɗe don daƙile ayyukan mugayen dabbobi a nan gaba.
Cikin rahoton binciken da suka wallafa, masana kimiyya sun ɗora wa jan macijin alhakin haifar da ɓarnar dala biliyan 10.3 jimilla - ta hanyar karaɗe wasu tsibirai a yankin Pacific.
A yankin Guam, inda sojojin Amurka suka ƙaddamar da macijin a ƙarnin da ya gabata, 'ya'yan nau'insa sun haddasa ɗaukewar wutar lantarki da yawa saboda suna maƙalƙalewa kan wayoyin lantarki tare da haddasa asara mai yawan gaske.
Akwai nau'in wannan maciji kusan aƙalla miliyan biyu a ɗan ƙaramin tsibirin, inda wasu alƙaluman ke cewa akwai aƙalla guda 20 a tsawon kowace girman eka na dajin Guam.
Ana ganin dazukan da ke tsibirai sun fi fuskantar hatsarin muggan dabbobi - inda suke yawan saka sauran dabbobin da ke rayuwa a wurin cikin haɗarin ƙarewa a ban-ƙasa.

Asalin hoton, Getty Images
A nahiyar Turai, akwai dandazon kwaɗi da ke buƙatar a kula da su da kyau.
Don daƙile haɗarin kwaɗin - waɗanda kan yi tsawon da ya kai na kusan ƙafa ɗaya da kuma nauyin rabin kilo - sun tilasta wa hukumomi dasa shingaye a wuraren kiwo.
Saka shinge a wuaren kiwo biyar kawai don hana kwaɗin guduwa ya jawo wa hukumomin Jamus kashe kuɗi yuro 270,000 - kwatankwacin naira miliyan 114, kamar yadda wani tsohon bincike na Tarayyar Turai ya bayyana.
Rahotanni na cewa dabbar na cin kusan komai, ciki har da 'yan uwansa kwaɗi.
Ana zargin wani nau'in na kwaɗo da aka fi sani da haddasa asara ta wata hanyar daban: ƙarar kukansu ta sa darajar gidajen da ke kusa da su ta karye.
Masu bincike na fatan sakamakon abin da suka gano zai ƙarfafa wa hukumomi gwiwa wajen samar da kuɗaɗen daƙile barazanar dabbobi mugaye.









