Abubuwa 15 da suka kamata ku sani kan firimiyar Najeriya ta 2023-24

An wallafa

A ranar Lahadi ne aka kammala gasar firimiyar Najeriya (NPFL) ta 2023-24 bayan buga jimillar wasa 370, kuma ita ce karo na 52 a tarihi.

Yayin da Rangers International ta zama gwarzuwar gasar, ƙungiyoyin Sporting Lagos, da Doma United, da Heartland, da Gombe United ne suka ƙare a ƙasan teburin gasar kuma suka sauka zuwa ƙaramar gasar NNL.

Ƙungiyoyin Remo Stars, da Enyimba ne za su wakilci Najeriya a gasannin zakarun Afirka na Caf Champions League da kuma Caf Confederations Cup.

Ga wasu abubuwa 15 da suka faru a gasar ta bana da aka kammala:

1 - Ɗan wasan Enyimba, Victor Mbaoma, shi ne kan gaba wajen jefa ƙwallaye a raga bayan ya ci 16.

2 - Ɗan wasan gaba na Kano Pillars, Yusuf Abdullahi, shi ne kaɗi ya ci ƙwallo sama da uku a wasa ɗaya - inda ya ci Gombe United ƙwallo biyar a wasan da suka yi nasara 5-2.

3 - 'Yan wasa shida ne suka ci ƙwallo uku rigis a wasa ɗaya a kakar bana. Su ne Robert Mizo (Bayelsa United), Yusuf Abdullahi (Kano Pillars), Albert Hillary (Plateau United), Nyima Nwagua (Rivers United), Silas Nenrot (Plateau United), Ubong Friday (Akwa United), Godwin Obaje (Plateau United).

4 - Remo Stars ce ta fi kowa karɓar jan kati a kakar bana, inda aka bai wa 'yan wasanta jan katin har sau bakwai - Enyimba ce ke biye mata da shida.

5 - Tun ana saura wasa ɗaya a gama gasar Rangers ta ɗauki kofin.

6 - Doma United da ta sauka daga gasar, ta fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da an zira mata ƙwallo a raga ba - da guda uku kawai ta ɗara zakarun gasar Rangers.

7 - Rangers sun fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da rashin nasara ba, inda ta jera wasa 10 ba a doke ta ba - ta ɗara Doma United da wasa ɗaya.

8 - Heartland - wadda ta sauka daga gasar - ita ce ta fi kowa yawan wasa a jere ba tare da nasara ba. Ta buga wasa 11 babu nasara, sai kuma Doma da Gombe da suka buga 10-10 a jere babu nasara.

9 - Ɗan wasan Plateau United, Silas Nenrot, shi ne ya ci ƙwallo uku rigis a mafi ƙanƙantar lokaci a bana. Ɗan wasan gaban ya ci cikin minti 11 a wasan da suka doke Gombe United 4-0 a wasan mako 25.

10 - An ba da jan kati sau 49.

11 - An buga finareti 90, inda aka ci 70 kuma aka ɓarar da 20

12 - An ci ƙwallaye 848

13 - Sau 29 ƙungiyoyoyi suka yi nasara a wasannin da suka buga a waje

14 - Gombe ce ta fi kowa ɗibar ƙwallaye, inda aka zira mata 76 jimilla.

15 - An buga canjaras a wasa 86