Van Dijk ba zai buga wasan Liverpool da Toulouse ba

Virgil van Dijk

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kyaftin ɗin Liverpool Virgil van Dijk ba ya cikin tawagar ƙungiyar da ta tafi Toulouse ba yayin da ta ke neman samun gurbin zuwa zagaye na gaba a gasar Europa League a ranar Alhamis.

Van Dijk na fama da rashin lafiya amma ana sa ran zai dawo cikin tawagar a wasan da za su yi da Brentford a gasar Premier ranar Lahadi.

Luis Diaz na cikin tawagar Klopp yayin da ake ci gaba da tattaunawa don kuɓutar da mahaifinsa daga hannun masu garkuwa da mutane a Colombia.

Sakamakon nasara uku da ta yi a wasanni uku na rukunin E, Liverpool za ta kai zagaye na gaba idan har ta sake doke Toulouse.

Idan Liverpool ta yi nasara kuma Union SG ba ta yi nasara a LASK ba, ƙungiyar Klopp za ta ci gaba da jan ragamar rukunin inda ya rage sauran wasanni biyu.

Ɗan wasan Netherlands Ryan Gravenberch ba zai samu buga wasan ba sakamakon rauni, hakan na nufin Wataru Endo zai iya farawa a tsakiya.