Everton da United na zawarcin Brown, Napoli na son tsawaita zaman Osimhen

Dan wasan Nijeruya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Victor Osimehin
An wallafa

Manchester United za ta iya rasa dan wasan bayan Faransa Raphael Varane, mai shekara 30,idan wa’adin kwantaraginsa ya kare a bazara mai zuwa . (Athletic - subscription required)

Barcelona da sauran manyan kungiyoyin kwallon kafar turai na zawarcin dan wasan gaban Manchester United da Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22 wanda a yanzu an bada shi aro ga Getafe. (Talksport)

Napoli ta tattauna da wakilan dan wasan gaba na Nijeriya ,Victor Osimhen game da tsawaita kwantaragin dan wasan mai shekara 24 har zuwa 2026, ciki har da kudin kusan fam miliyan £115m. (Sky Sports Italy)

Kocin Manchester United Erik ten Hag ba ya cikin hadarin rasa aikinsa yayin da kulob din ba ya son ya yanke shawara game makomarsa har sai bayan an kamala cinikin sayar da kashi 25 cikin 100 na kungiyar ga kamfanin Ineos na Sir Jim Ratcliffe . (Independent)

Sai dai tsohon kocin Chelsea da Brighton Graham Potter na cikin wadanda Manchester ta ke zawarci domin maye gurbin Ten Hag. (Sun)

Tsohon kocin-Wolves Julen Lopetegui shi ma yana cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin dan kasar Netherlands din,

AC Milan na tattaunawa da Arsenal kan batun aro mai tsaron bayan Poland Jakub Kiwior mai shekara 23 . (Calciomercato - in Italian)

Dan wasan bayan Borussia Monchengladbach da Switzerland Nico Elved mai shekara 27, ya kasance wanda Chelsea ke son dauka a watan Janairu sakamakon raunin da dan wasan Ingila Reece James mai shekara 24 ya sake ji . (Teamtalk)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin samun damar shiga gasar cin kofin Zakarun Turai da Manchester United ta yi ya haifar da gibi a cikin kasafin kudinta na zunzurutun kudi har fam milian 28 na cefanar da ‘yan wasa , kuma wannan na nufin cewa kofofinta a bude suke ga kungiyoyin da ke son su dauki dan wasan tsakiya dan kasar Brazil Casimero mai shekara 31 da mai kai hari dan kasar Faransa Anthony Martial mai shekara 28 da kuma Varane. (Mail)

Chelsea a shirye ta ke ta saurari tayin da aka yi wa dam wasan gefe dan kasar Netherlands Ian Maatsen, mai shekara 21, a kasuwar sayar da ‘yan wasa ta watan Janairu . (Mirror)

Watakila Aston Villa ta dauko dan wasan tsakiya Red Bull Salzburg da Israila Oscar Gloukh mai shekara 19 a watan Janairu akan kudi fam miliyan i50m. (Football Insider)

Wolves ta amince da sabuwar yarjejeniya kan dan wasan gaba Koriya ta Kudu Hwang Hee-chan, mai shekara 27, har zuwa 2028 (Fabrizio Romano)

Everton, da Burnley da Leeds United na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan bayan Ingila Archie Brown mai shekaa 21 da ke tala leda Gent. (Mail)