Yadda ƴan bindiga ke karban haraji daga 'yan gudun hijira a Neja

Asalin hoton, Getty Images
Mazauna wasu yankunan jihar Naija, da ke arewa ta tsakiyar Najeriya na ci gaba da yin gudun hijira sandiyyar hare-haren 'yan bindiga da ke tursasa musu biyan haraji.
Bayanan da BBC ta samu na nuna cewa wannan lamari ya shafi al'ummomin da ke zaune a garuruwan da suka hada da Dagon -dawa da Kurigi da Kangerawa da Mangoro da wasu da dama.
Wasu mazauna wadannan garuruwa sun shaida mana cewa 'yan bindigar na tursasa musu biyan haraji a kan kayan abinci, da kuma zirga-zirga da aikin gona.
''Nan gabas gare me, daga bakin Kurege zuwa Dogon Dawa, abun ya yi tsanani, har ta kai ga masu gudun hijirar da ke neman guduwa ma yanzu yan bindiga na tare su da sunan sai sun biya haraji kafin su fice, don haka sai ka biya kudi za ka samu damar yin gudun hijirar ma'' In ji wani mazaunin garin Dogon Dawa, da muka sakaye sunansa saboda dalilan tsaro.
Ya ce a halin da ake ciki 'yan bindigar sun mayar da wadannan garuruwa tamkar wani yankinsu, inda suke harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.
'Abun da muke biya a matsayin kudin fansa'
Wasu mazauna wadannan garuruwa sun shaida wa BBC cewa 'yan binidgar na cazar Naira dubu dari biyu ko dubu dari uku ga kowacce mota da ta dakko kayan yan gudun hijira kafin su ba ta damar wucewa, wani lokacin su hada motoci uku su ce a basu miliyan daya
'Ko ranar Lahadi sai da aka kai musu Naira miliyan uku da rabi na wasu motoci da suka dakko kayan yan gudun hijira, suka ce ba za su wuce ba sai an biya su wannan kudin' inji wani da muka zanta da shi.
Shima wani da muka zanta da shi ya ce ''An hada motoci za a je a dakko abinci, kusan kantoci 29, an lodo kayayyaki amma suka hana mu wucewa suka ce kowacce mota sai an biya Naira dubu dari biyu, kuma haka aka yi''
BBC ta yi kokarin jin ta bakin mahukunta a jihar ta Naija, sai dai hakanmu bai cimma ruwa ba.
Batun biyan haraji da 'yan bindiga ke tursasa wa mutane yi dai ba sabon abu bane a Najeriya musamman a garuruwan da ke fama da matsalolin yan fashin daji, inda 'yan bindigar ke tursasa biyan wasu kudi kafin samun damar gudanar da wasu sha'anonin rayuwa musamman ma noma.










