Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Roma ta kori Mourinho ta maye gurbinsa da De Rossi
Roma ta raba gari da Jose Mourinho ta maye gurbinsa da tsohon ƙyaftin dinta, Daniele de Rossi.
Mourinho, mai shekara 60, ya karbi aiki a Mayun 2021, wanda ya ja Roma ta dauki Europa Conference League da zuwa wasan karshe a Europa League a 2023.
Sai dai kungiyar tana mataki na tara a teburin Serie A da tazarar maki biyar tsakaninta da gurbin Champions League a yanzu haka.
A makon jiya ne aka yi waje da ita a Coppa Italiya a hannun abokiyar hamayyarta Lazio.
Tsohon dan kwallon Roma, De Rossi ya maye gurbin Mourinho zuwa karshen kaka bana.
Zakakurin dan ƙwallon ƙungiyar mai shekara 40, ya fara wasa daga ƙaramar Roma, wadda ya yi wa wasa 616 tsakanin 2001 zuwa 2019 a babbar kungiyar.
De Rossi ya yi ritaya a 2020 daga lokacin ya koma aikin horar da tamaula - ya ja ragamar wasa 17 a SPAL a Serie B, wadda ta kore shi a Fabrairun 2023.
De Rossi, ya buga wa tawagar Italiya wasa 117 da lashe kofin duniya a 2006.
Roma tana mataki na 16 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Italiya ta bana.
Tsohon kociyan Manchester United da Chelsea da Real Madrid da kuma Tottenham ya ce ya samu tayin kwantiragi mai tsoka na barin kungiyar kan fara kakar bana, amma ya zabi ci gaba da zama a Roma.
Tun farko sai a karshen kakar nan yarjejeniyar Mourinho ya kamata ya kare.