Wani biloniya na son sayen Manchester United

Sir Jim Ratcliffe hamshakin mai kudi ne a Burtaniya

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Biliniyan Burtaniya nan Sim Jim Ratcliffe na son sayan Manchester United.

Labarin cewa mai kudin dan shekara 69 ya fito daga jaridar Bloomberg ne biyo bayan sha’awar da ya nuna ta sayan wani bangare ga kungiyar, bayan da iyalan Glazer suka nuna sayar da wani abu daga cikin hannun jarinsu.

“Idan har da gaske sayar da kungiyar za a yi to fa Jim a shirye yake ya saye ta” in ji kakakin Ratcliffe.

Ya shaida wa jaridar The Time cewa, “idan har wannan abu ne mai yiwuwa, muna da sha’awar sayan shiyyar na dogon lokacin.”

Kungiyar wadda ta lashe Premier sau 20, tana karshen teburin gasar a wannan karon bayan rashin nasara da ta yi a wasanni biyun farko na gasar da aka fara ba dadewa karkashin sabon kocinta Erik ten Hag.

Mummunan sakamakon fara gasar da ta yi, ya sanya an ta sukar iyalan na rashin zuba kudi a kungiyar yadda ya kamata.

A wannan kakar United ta yi ta kokarin sayan yan wasa masu kyau amma abin yana cin tura, ciki har da dan wasan Barcelona dan kasar Netherland  Frenkie de Jong da kuma yiwuwar ficewar Cristiano Ronaldo.

Tun bayan ritayar da Sir Alex Ferguson a 2013 United ke ta fadi tashi, kuma ba ta ci kofi ko day aba tun 2017.

An ta fama da zanga-zangar nuna kin jinin yadda iyalan Glazer ke tafiyar da kungiyar a yan shekarun nan, ciki har da wadda aka yi a watan Mayun 2021 wadda ta janyo aka dage wasan United da Liverpool.

A yanzu ma haka sun shirin tsara wata zanga-zangar ga iyalan na kasar Amurka yayin wasan da za ta buga a Old Trafford da abokiyar hamayyarta ta Anfield.