Crystal Palace ta kori Patrick Vieira

Patrivk Vieira

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Crystal Palace ta sallami kociyanta, Patrick Vieira, bayan da ya kasa cin wasa 12.

Palace ba ta ci wasa ba a 2023, wadda Brighton ta doke 1-0 a Premier League ranar Laraba, karo na uku da ta yi rashin nasara a jere.

Kungiyar tana ta 12 a teburin Premier League, amma tazarar maki uku ne kacal tsakaninta da ta ukun karshen teburi, wato wadda take ta 18. Bournemouth.

Palace ta nada Vieira dan kasar Faransa aiki, mai shekara 46 kafin fara kakar 2021/22, wanda ya kai kungiyar mataki na 12 a bara.

An yaba wa Vieira kan yadda ya sauya salon wasannin Palace ta zama mai hadari da kai hare-hare da taka rawar gani a fagen taka leda.

Sai dai a kakar nan sun ci kwallo 21 a wasa 27 - wadanda suka ci karancin kwallaye a kakar nan sune Wolves da Everton da kuma Southampton.

Kafin Brighton ta ci Palace ranar Laraba, kungiyar ta yi karawa uku a jere ba tare da yin nasara ba, sannan ba ta kai wani mummunan hari ba.

Palace ce kadai mai karancin maki a 2023, mai biyar daga 33 da ya kamata ta samu.

Masu taimaka wa Vieira uku wato Osian Roberts da Kristian Wilson da kuma Said Aigoun sun bar kungiyar.

Palace za ta ziyarci Arsenal a wasan hamayya a gasar Premier League ranar Lahadi a Emirates.

Cikin wasa 10 na karshe da Palace za ta buga za ta fafata da kungiyoyin da ke kasa-kasan teburi, kenan za ta fuskanci kalubale da yawa.

Vieira tsohon da kwallon Arsenal ya kai Palace karawar daf da karshe a FA Cup a Wembley da kuma kai kungiyar mataki na 12 a teburin Premier a bara.

Rabon da Palace ta ci wasa tun jajiberin sabuwar shekara da ta doke Bournemouth.