Hotunan ziyarar Shugaba Buhari a Maiduguri

An wallafa

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kai ziyara birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar, ranar Alhamis 18 ga watan Agustan 2022.

Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ta yi fama da ricikin Boko Haram, abin da ya sa dubban jama’a suka shiga mawuyacin hali.

Wannan dai ita ce ziyara ta uku da shugaban ya kai jihar Borno cikin shekara guda.

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na yadda ziyarar ta kasance.