Hotunan ziyarar Shugaba Buhari a Maiduguri

An wallafa

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kai ziyara birnin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin ƙasar, ranar Alhamis 18 ga watan Agustan 2022.

Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ta yi fama da ricikin Boko Haram, abin da ya sa dubban jama’a suka shiga mawuyacin hali.

Wannan dai ita ce ziyara ta uku da shugaban ya kai jihar Borno cikin shekara guda.

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na yadda ziyarar ta kasance.

Buhari a Maiduguri

Asalin hoton, Presidency

Buhari a Maiduguri

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Ma'aikatar jin ƙai da ci gaban al'umma da kare aukuwar bala'i ce ta gayyaci Shugaba Buhari, a wani ɓangare na bikin ranar jin ƙai ta duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da gidajen malaman makaranta da aka kammala aikinsu.

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da gidajen malaman makaranta da aka kammala aikinsu.
Gidajen Malamai a Maiduguri

Asalin hoton, Borno Govt

Bayanan hoto, Rukunin gidajen malamai da gwamnatin Borno ta gina a Bulumkutu na daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar
Shugaba Buhari na sauka daga jirgi

Asalin hoton, Borno Govt

Bayanan hoto, Wannan ita ce ziyara ta uku cikin shekara guda da Shugaba Buhari ke kai wa jihar Borno.
Shugaba Buhari a fadar Shehun Borno

Asalin hoton, Borno Govt

Bayanan hoto, A daya daga cikin ziyarar da shugaban ya kai jihar Bornon ne ya bayar da umarnin gina gidaje 10,000 don tsugunar da ƴan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Buhari a Borno

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Kuma a ziyarar wannan karon Shugaba Muhammadu Buharin ya ƙaddamar da 500 daga cikinsu.
Buhari a Borno

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Hukumomin jihar Borno sun ce za a kammala gina gidaje 6,000 ɗin nan ba da jimawa ba.