Timber zai je wajen kwararru don fayyace girman raunin da ya ji

Jurrien Timber

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan kwallon Arsenal, Jurrien Timber zai je wajen kwararru domin su auna girman raunin da ya ji a gwiwar kafarsa.

Dan wasan ya ji rauni a wasan Premier League ranar Asabar da Arsenal ta ci Nottingham Forest 2-1.

Dan kwallon tawagar Netherlands ya koma Gunners daga Ajax kan fam miliyan 38.5, an kuma sauya shi a zagaye na biyu a karawar.

Wasu rahotannin na cewa raunin da Timber ya yi zai iya zama mai muni da wasu ke cewa zai iya jinya har zuwa farkon 2024.

Ranar Litinin Arsenal ta sanar cewar za a kara auna girman raunin Timber, domin tantance ranar da ya kamata ya koma taka leda.

Tun kan nan Gunners ta ce bayan da aka sauya dan kwallon a karawa da Forest ta sa likitoci sun auna koshin lafiyarsa, wadanda suka fayyace irin ciwo da ya ji.

Saboda haka Timber zai ziyarci kwararru domin fayyace girman raunin da ya ji da tabbatar da ranar da zai koma taka leda a Gunners.