Man Utd na son ɗauko Kane, Chelsea za ta yi gwanjon ƴanwasa 15

Harry Kane

Asalin hoton, PA Media

An wallafa

Sabon mai hannun jarin Manchester United Sir Jim Ratcliffe na shirin amincewa da buƙatar kashe fam miliyan 100 domin ɗauko ɗanwasan Benfica da Portugal Joao Neves mai shekara 19. (Mirror, via Mail)

United za ta yi ƙoƙarin ɗauko ɗanwasan gaba na Bayern Munich da Ingila Harry Kane, mai shekara 30 idan har yana kasuwa a bazara. (Give Me Sport)

Liverpool ta lissafa kocin Brighton Roberto de Zerbi da na Jamus Julian Nagelsmann da na Sporting Lisbon Ruben Amorim cikin jerin waɗanda take nazarin za su maye gurbin Jurgen Klopp. (Football Insider)

Ɗanwasan tsakiya na Jamus Joshua Kimmich, wanda Manchester United da Manchester City da Liverpool ke ribibinsa har yanzu bai tattauna ba da Bayern Munich game da makomarsa yayin da ya rage wata 18 kwangilarsa ta kawo ƙarshe. (90min)

Arsenal na son sayar da ɗanwasan bayanta Kieran Tierney a bazara amma kuma tana son a biya ta fam miliyan 20 kan ɗanwasan na Scotland mai shekara 20. (Give Me Sport)

Chelsea har yanzu ba ta yanke hukunci ba kan makomar ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 24 Conor Gallagher da ake alaƙantawa da Tottenham. (Caught Offside)

Chelsea za ta yi gwanzon ƴanwasa da dama kusan 15 idan an buɗe kasuwar ƴanwasa a bazara. (Football.London)

Manchester United na son lunka albashin ɗanwasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, ƙasa da shekara ɗaya bayan ya sabunta yarjejeniyarsa domin tana son ya ci gaba da taka leda har zuwa 2030. (Sun)

AC Milan na ci gaba da tattaunawa da Arsenal kan ɗanwasan baya na Poland Jakub Kiwior, mai shekara 24. (Fichajes, via Team Talk)