Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun kaɗu da jin cewar Klopp zai bar Liverpool - Van Dijk
Virgil van Dijk ya ce sun kadu da jin cewar Jurgen Klopp ya yanke shawarar ajiye aikin horar da Liverpool daga ƙarshen kakar bana.
Ranar Juma'a Klopp dan kasar Jamus ya sanar cewar zai yi ritaya daga aikin kociyan, Liverpool a karshen watan Yulin kakar nan.
Tun cikin watan Nuwamba ya sanar da mahukuntan kungiyar kan shawarar da ya ɗauka, amma sai a ranar Juma'a aka sanar da ƴan wasa.
''Mahukuntan kungiyar sun kwan da sanin mahimmacinsa a gare ni da kuma kungiyar,'' in ji kyaftin, Van Dijk.
''To amma ya riga ya yanke shawara mafi alheri a wajensa da iyalansa. Wannan batu ne mai tsauri, zai ci gaba da kasancewa a hakan.
''Ya fada mana a lokacin da muka kebe. Har yanzu muna da buruka da muke fatan cimma tare da shi, me zai hana mu karasa kakar nan da yin abin kirki, domin taya kociyan mu murna?''
Van Dijk ya koma Liverpool a tsakiyar kakar tamaula lokacin da Klopp ke shekara uku da aikin kociyan kungiyar, wanda kawo yanzu ya lashe kofi shida tare da dan kasar Jamus mai shekara 56.
Har yanzu Liverpool tana cikin takarar lashe kofi hudu a bana, bayan da ta kai wasan karshe a gasar Leage Cup da za ta kara da Chelsea.
Sannan ƙungiyar na mataki na farko a teburin Premier League, tana kuma buga Europa League da kuma FA Cup a kakar nan.