Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles za ta buga wasan sada zumunta da Ghana da Mali
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta sanar cewar za ta buga wasan sada zumunta da Ghana da Mali a Morocco cikin watan Maris.
Shi ne babban wasa da Super Eagles za ta kara tun bayan da Ivory Coast ta doke ta 2-1 a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka cikin watan Fabrairu.
Super Eagles za ta fara wasa da Ghana ranar 22 ga watan Maris, sannan kwana hudu tsakani ta fafata da Mali a birnin Marrakech da ke Morocco.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da wasannin sada zumuntar biyu da za ta buga a watan gobe a shafinta na sada zumunta X.
Wasa tskanin Super Eagles da Black Stars yana jan hankalin 'yan kallo, domin hamayyar da ke tsakanin tawagogin biyu.
Ghana dai ba ta kai bante ba a gasar cin kofin Afirka da aka yi a Ivory Coast, wadda aka fitar daga karawar cikin rukuni.
Tuni kuma Najeriya ta bayyana 'yan wasan da ta gayyata, domin buga mata wasan biyu a cikin watan Maris, lokacin da Fifa kan ware don buga irin wadan nan karawar.
Cikin 'yan wasan Super Eagles, William Troost-Ekong, wanda ke jinya ba zai buga fafatawar ba.
To sai dai an gayyaci Taiwo Awoniyi da Sadiq cikin tawagar, bayan da rauni bai bari sun buga wa Super Eagles gasar cin kofin Afirka ba.