Senegal ta sadaukar da nasararta ga marigayi Papa Bouba Diop

Senegal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

'Yan wasan kasar Senegal sun sadaukar da nasararsu a kan Ecuador ga marigayi tsohon dan kwallon kasar, Papa Bouba Diop, wanda ya buga gasar Kofin Duniya a 2002.

Nasarar Senegal da ci biyu da daya a kan Ecuador ita ce ta ba ta damar kai wa zagaye na biyu kuma za ta hadu da Ingila a ranar Lahadi mai zuwa.

Nasarar ta zo shekaru biyu cif bayan rasuwa dan kwallon, wanda ya mutu yana da shekaru 42.

Diop ne ya zura kwallon da ta bai wa Senegal nasara a kan Faransa a wasan farko na gasar cin Kofin Duniya shekaru 20 da suka wuce.

Kyaftin din Senegal Kalidou Koulibaly ya sanya kambum kyaftin dauke da lamba 19 watau lambar da Diop ne ke sakawa.

"Mun karrama shi ne kasancewarsa gawurtaccen dan kwallon," in ji Koulibaly.

Diop ya taimaka wa Senegal kai wa zagayen gab da na kusa da karshe a Japan da Koriya ta Kudu.

Kasashen Afrika biyu ne kawai suka taba kaiwa zagayen gab da da kusa da karshe a gasar cin Kofin Duniya, watau Senegal da Kamaru.