Ronaldo zai zama na farko da zai buga Euro karo na shida

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Cristiano Ronaldo zai zama na farko da zai buga gasar cin kofin nahiyar Turai wato Euro karo na shida a tarihi.

Portugal za ta yi wasan farko a rukuni na shida da Jamhuriyar Czech, inda ake sa ran Ronaldo zai buga wasan da zai kafa tarihi a Jamus Euro 2024.

Kawo yanzu mai rike da Ballon d'Or biyar ya yi wasa 25 jimilla da cin kwallo 14 a babbar gasar tamaula ta cin kofin nahiyar Turai.

Mai shekara 39 tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus ya lashe kofi daya da tawagar Portugal, shi ne Euro 2016.

Ronaldo ya fara buga Euro a karawar da Portugal ta yi da Girka, wanda ya ci kwallo a fafatawar ranar 12 ga watan Yunin 2004.

A Euro 2026, kyafrin tawagar Portugal ya yi kan-kan-kan da Michel Platini a yawan cin kwallaye da yawa a gasar mai tara a raga.

Sai dai kuma a Euro 2020, Ronaldo ya haura tsohon dan wasan tawagar Faransa da cin kwallo biyar, jimilla da 14 ba wanda ya kai shi wannan bajintar.

Jerin wadanda ke kan gaba a yawan cin kwallaye a Euro

  • Cristiano Ronaldo (Portugal) kwallo 14
  • Michel Platini (France) kwallo 9
  • Alan Shearer (England) kwallo 7
  • Antoine Griezmann (France) kwallo 7
  • Álvaro Morata (Spain)
  • Ruud van Nistelrooy (Netherlands) kwallo 6
  • Patrick Kluivert (Netherlands) kwallo 6
  • Wayne Rooney (England) kwallo 6
  • Thierry Henry (France) kwallo 6
  • Zlatan Ibrahimović (Sweden) kwallo 6
  • Nuno Gomes (Portugal) kwallo 6

Ana buga Euro duk bayan shekara hudu, an samu tsaiko a Euro 2020, sakamakon bullar cutar korona, wadda aka yi tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yulin 2021.

Tuni kuma Ronaldo ya yi gasa biyar babu dan kwallon da ya buga Euro da yawa kamar shi, wanda ke fatan buga gasa ta shida a Euro 2024 a Jamus.

Jerin wadanda suka buga Euro da yawa a tarihi

  • Cristiano Ronaldo, Portugal (2004, 2008, 2012, 2016, 2020)
  • Luka Modrić, Croatia (2008, 2012, 2016, 2020)
  • Lothar Matthäus, West Germany/Germany (1980, 1984, 1988, 2000)
  • Peter Schmeichel, Denmark (1988, 1992, 1996, 2000)
  • Alessandro Del Piero, Italy (1996, 2000, 2004, 2008)
  • Edwin van der Sar, Netherlands (1996, 2000, 2004, 2008)
  • Lilian Thuram, France (1996, 2000, 2004, 2008)
  • Olof Mellberg, Sweden (2000, 2004, 2008, 2012)
  • Gianluigi Buffon, Italy (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Petr Čech, Czech Republic (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Zlatan Ibrahimović, Sweden (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Andreas Isaksson, Sweden (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Kim Källström, Sweden (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Jaroslav Plašil, Czech Republic (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Lukas Podolski, Germany (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Tomáš Rosický, Czech Republic (2000, 2004, 2012, 2016)
  • Bastian Schweinsteiger, Germany (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Darijo Srna, Croatia (2004, 2008, 2012, 2016)
  • Giorgio Chiellini, Italy (2008, 2012, 2016, 2020)
  • Sebastian Larsson, Sweden (2008, 2012, 2016, 2020)
  • Luka Modrić, Croatia (2008, 2012, 2016, 2020)
  • João Moutinho, Portugal (2008, 2012, 2016, 2020)
  • Pepe, Portugal (2008, 2012, 2016, 2020)
  • Toni Kroos, Germany (2012, 2016, 2020, 2024)
  • Manuel Neuer, Germany (2012, 2016, 2020, 2024)
  • Thomas Müller, Germany (2012, 2016, 2020, 2024)
  • Ivan Perišić, Croatia (2012, 2016, 2020, 2024)