Koulibaly na daf da komawa Chelsea daga Napoli

Kalidou Koulibaly

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea na daf da daukar dan kwallon tawagar Senegal, mai tsaron baya, Kalidou Koulibaly daga Napoli kan yarjejeniyar kaka hudu.

Mai shekara 31 na daf da zuwa Los Angeles ranar Laraba idan an auna koshin lafiyarsa, domin ci gaba da atisaye tare da kungiyar Stamford Bridge.

Haka kuma Chelsea na ta kokarin sayen dan kwallon Manchester City, Nathan Ake.

'Yan wasan biyu za su dinke barakar gurbin masu tsaron bayan kungiyar bayan, bayan da Antonio Rudiger ya koma Real Madrid, ita kuwa Barcelona ta dauki Andreas Christensen.

Ranar Laraba Chelssea ta sanar da daukar dan kwallon Ingila, Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50.

Koulibaly, wanda kungiyoyin Premier League da dama ke son dauka, ya koma Napoli daga Genk a 2014, ya kuma yi wasa 317 a kungiyar da ke buga gasar Serie A.

Chelsea na yin atisayen tunkarar kakar bana a Amurka, inda Sterling ka iya buga mata wasan sada zumunta da za ta yi ranar Asabar a Las Vegas da Club America.

Daga nan kuma ta fuskanci Charlotte FC ranar Laraba, sannan ta kece raini da Arsenal ranar 23 ga watan Yuli.