Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League
Arsenal ta ci Leicester City 1-0 a wasan mako na 25 a gasar Premier League ranar Asabar.
Gabriel Martinelli ne ya ci wa Gunners kwallo a karawar da ta fuskanci kalubale mai zafi a King Power.
Dan wasan tawagar Brazil ya ci kwallon ne, bayan da aka koma zagaye na biyu, bayan da ya samu tamaula daga wajen Leandro Trossard ya buga ta wuce Danny Ward.
Arsenal mai kwantan wasa ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier da tazarar maki biyu tsakaninta da Manchester City, wadda ta doke Bournemouth 4-1 ranar Asabar.
Leicester City, wadda ta fara kakar bana da sassarfa tana ta 14 a kasan teburi.
Arsenal na fatan lashe kofin Premier League a karon farko tun bayan 2003-04 karkashin Arsene Wenger.