Ɗan wasan Man United Van de Beek na daf da komawa Girona

Donny van de Beek

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ɗan wasan Manchester United, Donny van de Beek na daf da komawa Girona da taka leda.

Van de Beek ya kasa nuna kansa tun bayan da ya koma Old Trafford kan £35m a Satumbar 2020.

Ɗan kasar Netherlands ya buga wasannin aro a Everton da kuma Eintracht Frankfurt a rabin kakar da ta wuce.

Wasu rahotanni na cewar Girona za ta biya ƙudin da zai kai £16.9m har da na tsarabe-tsarabe.

United za ta matukar ƙaru da cinikin, idan ya koma ƙungiyar da ke buga La Liga.