Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Indiya ke kai wa wata kungiyar Musulunci samame?
Wata kungiyar Musulmai ta Popular Front of India PFI mai janyo ce-ce-ku-ce a Indiya, na gudanar da zanga-zanga a jihar Kerala ranar Juma’a.
An yi hakan ne kwana guda bayan da hukumomin kasar suka kaddamar da samame a ofisoshin kungiyar da dama a fadin kasar, tare kuma da yin awon-gaba da shugabanninta
Me muka sani game da kungiyar? Me kuma ya janyo samamen?
Babbar hukumar yaki da ta‘addanci ta kasar NIA, tare da hukumar ED take yaki da laifukan da suka shafi kudi ne suka kaddamar da samamen a fadin jihohin kasar 11 ranar Alhamis da safe.
Aka kuma kame mambobin kungiyar 106, kamar yadda kafar yada labarai ta PTI ta kasar ta ruwaito.
Gidan talbijin na News18, ya ambato wata majiya daga hukumar ta NIA na cewa "samamen na daga cikin wani babban bincike da hukumar ta faro da dadewa.
Ranar Juma’a ne dai mambobin kungiyar suka gudanar da zanga-zanga kan adawa da kamen da hukumomin suka yi wa shugabanninta a kudancin jihohin Kerala da Tamil Nadu.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta zargi gwamnati da kokarin amfani da hukumomi domin tauye ‘yancin marasa galihu.
Sanarwar ta kara da cewa "Ana kai samamen a gidajen shugabannin kungiyar na kasa da na jihohi da kuma na kananan hukumomi."
A wata sanarwa da hukumar NIA ta fitar ga manema labarai ta ce ta kama mambobin kungiyar 45 saboda zarginsu kan wasu batutuwa biyar.
Hukumar ta ce a lokacin binciken jami’anta sun yi awon-gaba da ‘’Wasu takardu masu alaka da aikata laifi, da kudade, da adduna da kuma wasu na’urori masu yawa."
Mece ce kungiyar PFI?
Kungiyar ta PFI – wadda aka kafa a shekarar 2006, ta bayyana kanta da cewa "kungiya ce mai zaman kanta wadda makasudin kafa ta, shi ne kare hakkin marasa galihu, tare da adawa da zalunci da kuma tauye hakkinsu."
Kungiyar ta kafu ne bayan da kungiyar ci-gaban kasar ta National Development Front (NDF) – wata kungiya mai janyo ce-ce-ku-ce da aka kafa a jihar Kerala shekaru kadan bayan rushe masallacin Babri a shekarar 1992 – ta hade da wasu kungiyoyi biyu daga kudancin jihar.
Nan da wasu shekaru masu zuwa, kungiyar PFI ka iya zama wata gawurtacciyar kungiya saboda yadda wasu kananan kungiyoyi ke ci gaba da yi mata mubaya’a.
A halin da ake ciki kungiyar PFI, wacce ke da dubban daruruwan magoya baya a jihohin Kerala da Karnataka, na ci-gaba da samun karbuwa a fiye da jihohin kasar 20.
Me yasa PFI ke janyo ce-ce-ku-ce?
A taken kungiyar da ta wallafa a shafinta na intanet, Kungiyar ta yi furucin cewa ta na so ne ta ‘’samar wa da al’umma mai cikakken ‘yanci, da wanzuwar adalci, tare da samun ingantaccen tsaro’’.
To sai dai gwamnati ta gabatar da jerin tuhume-tuhume kan kungiyar tare da mambobinta, wadanda suka hadar da ‘’laifin tunzura al’umma, da yin kalaman nuna kiyayya da gaba tsakanin al’umomi, tare da kama hanyar wargaza Indiya’’.
An zargi mambobin kungiyar da laifin fille kan wani dan addinin Hindu a yammacin jihar Rajasthan a watan Yuni.
A ‘yan watannin da suka gabata, ‘yan sanda a gabashin jihar Bihar sun yi ikirarin cewa kungiyar na yada wasu takardu da ke maganar mayar da Indiya kasar Musulunci.
Zarge-zargen da kungiyar ta musanta, tana mai cewa takardun ba na gaskiya ba ne kirkirarsu a ka yi tare da danganta su da kungiyar.
Daya daga cikin manyan zarge-zargen da ake yi wa kungiyar shi ne alaka da haramtacciyar kungiyar IS, da kungiyar dalibai Musulmai ta Indiya (Simi), wadda gwamnati da haramta a shekarar 2001.
Haka kuma ana zargin kungiyar da laka da kungiyar Mujahideen wata kungiyar ‘yan ta’adda da itama gwamnati ta haramta.
Farfesa P Koya, wanda shi ne ya kafa kungiyar ta PFI ya musanta duka zarge-zargen tun da farko a wata tattaunawa da ya yi da BBC.
A tattaunawar ya ce ya kafa kungiyar NDF a shekarar 1993, shekaru bayan da ya yanke alaka da kungiyar Simi a shekarar 1981.
A shekarar 2010 ne aka fara nuna yatsa kan kungiyar bayan wani farmaki da aka kai wa Farfesa TJ Joseph a jihar Kerala.
Lamarin ya zo ne bayan da kungiyoyin Musulunci da dama suka zarge shi da laifin yin tambayoyin da ke kaskantar da darajar Annabi Muhammad SAW a lokacin wata jarrabawa.
Kotu ta kama wasu daga cikin ‘ya’yan kungiyar da laifin farmakin, koda yake kungiyar ta nesanta kanta game da wannan zargi.
A shekarar 2018 an zargi ‘yan gwagwarmayar kungiyar PFI da laifin daba wa wani shugaban daliban jihar Kerala wuka, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Yaya karfin kungiyar PFI yake?
Shugabannin kungiyar PFI sun jan hankulan kafofin yada labarai game da maganganun da wasu ke kallo a matsayin tunzuri.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa tana da dimbin mabiya a jihar Kerala, to sai dai ba ta samun ci gaba ta fannin siyasa.
Tana da jam’iyyar siyasa da ta yi wa rajista mai suna Social Democratic Party of India (SDPI), wacce ta shiga zabukan jihar, ta kuma samu kwarya-kwaryar nasara a jihar, ko da yake ba ta samu ko kujera daya a majalisar dokokin kasar.
Farfesa Adil Mehdi tsohon malami ne a Jami’ar Musulunci ta Jamia Millia da ke birnin Delhi, ya ce ‘’kungiyar PFI ba wata kungiya ba ce mai karfi a Indiya.
Duka-duka tasirinta bai wuce jihar Kerala da wasu jihohin kudancin kasar.
Musulmai da yawa da ke zaune a wasu yankunan Indiya ba su ma san da ita ba a matsayin jam’iyyar Siyasa’’.
A farkon shekarar nan ne, gwamnatin jihar Karnatakata zargi kungiyar PFI da rura wutar zanga-zanga, bayan da wata makaranta a jihar ta hana dalibai mata sanya hijabi.
Masu sanya ido sun ce kungiyar mata da dalibai reshen kungiyar ne ke kan gaba a zanga-zangar da aka gudanar a fadin kasar.
Kungiyoyin kishin addinin Hindu tare da hadin gwiwwar jam’iyyar BJP mai Mulki, sun dade suna kiraye-kirayen haramta kungiyar PFI.
Haka kuma babbar kotun Kerala ta taba ayyana kuniyar PFI a matsayin kungiyar ‘’masu kaifin kishin addini."
Kungiyar PFI na ci gaba da musanta alaka da ayyukan ta’addanci, sannan kuma masu sharhi na ganin cewa tuhumar alaka da ta’addanci da ake yi wa kungiyar - wanda shi ne ya haddasa samame tare da kamen da aka yi wa ‘yan kungiyar - ba ta da tushe balle makama.