Chelsea ta ci wasa karon farko bayan canjaras uku da duro uku

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta yi nasara a kan Leeds United da cin 1-0 a wasan mako na 26 a Stamford Bridge a gasar Premier League.

Welsey Fofana ne ya ci kwallon kuma na farko a Premier League, hakan ka iya rage matsin da koci, Graham Potter ke fuskanta.

Chelsea wadda ta yi wasa 15 a baya ta yi nasara a biyu daga ciki har da wanda ta doke Crystal Palace 1-0 ranar 15 ga watan Janairu a Stamford Bridge.

Tun daga lokacin ta yi canjaras uku da rashin nasara a karawa uku a dukkan fafatawa har da 1-0 da Dortmund ta doke ta a Jamus a Champions League.

A karawa da Leeds ranar Asabar Chelsea ta nuna da gaske take wadda ta barar da damar makin cin kwallo, musammam guda uku a cikin minti 30.

The Blues made a blistering start and could have been 3-0 up inside 30 minutes.

Kai Havertz ya yi gaba da gaba da golan Leeds, Illan Meslier, Joao Felix ya buga wata kwallo mai kyau, wadda ta doke turke, Ben Chilwell ya taba ta yi fadi.

Da wannan sakamakon Chelsea ta ci gaba da zama a mataki na 10 a teburin Premier, Leeds kuwa tana ta 17 da tazarar maki daya tsakaninta da 'yan ukun karshe

Ranar 7 ga watan Maris, Chelsea za ta karbi bakuncin Borussia Dortmund a wasa na biyu zagayen 'yan 16 a Champions League a Stamford Bridge.

Kwana hudu tsakani kungiyar Stamford Bridge za ta ziyarci Leicester City a King Power domin buga Premier League