Dalilin da ya sa ake ganin Yarima Harry ya fi samun goyon bayan Amurkawa fiye da 'Yan Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images
Babu shaka Amurkawa sun yi yaƙin neman ƴancin kai daga Birtaniya domin cire kansu daga mulkin mallakar da ake yi musu, sai dai da alama har yanzu sun kasa rabuwa da shiga harkokin da suka shafin Masarautar Birtaniya.
A halin yanzu da dama daga cikin Amurkawan hankalinsu ya karkata matuƙa kan irin diramar da ake yi a gidan Gidan Sarautar Birtaniya da ta shafi Yarima Harry da matarsa Meghan.
Harry da Meghan na da waɗanda suke caccakarsu a Amurka - sai dai ba su kai yawan waɗanda ake da su a Birtaniya ba.
A Amurkar, labarin yadda gidajen jaridar Birtaniya da kuma gidan sarautar ƙasar ya rinƙa musguna wa ma'auratan ya zama abin tausayi ga Amurkawan.
Ɗaya daga cikin ƙorafin da ma'auratan suka rinƙa yi shi ne yadda aka rinƙa takura musu a gidan sarautar.

Asalin hoton, Getty Images
A wata tattaunawa da Meghan ta yi da mujallar The Cut, ta bayyana cewa zamansu na ma'aurata ita da mijinta suna kawo cikas ga gidan sarautar.
Harry ya yi ƙorafin cewa shi da matarsa an miƙa su ga ƴan jarida sakamakon gidan sarautar na so ya kare wasu manyan ƴan Gidan Sarautar Birtaniya.
Tsarin da ake amfani da shi na matsayi ko mataki a Gidan Sarautar Birtaniya wanda ake la'akari kan mutum ko shi na nawa ne a gidansu an fahimce shi tsawon shekaru a Birtaniya.
A Amurka hakan ba wai ya kasance wani sabon abu ba ne a gare su, sai dai suna kallon lamarin kamar wani abu na rashin imani.
Martanin da Amurka ta yi na mayar kan rasuwar Sarauniya Elizabeth II ya nuna cewa akwai girmamawa da kuma ƙauna ga masarautar.
Sai dai ba lallai hakan bane abin da ake so a ko wane yanki.

Asalin hoton, Getty Images
Ga Amurkawa, sun fi ganin cewa dukiyar Masarautar Birtaniya ta samo asali ne daga wadda suka samu a lokacin mulkin mallaka.
A lokacin da Amurka ke ta ƙoƙarin koyawa da kuma fahimtar da irin mummuna tarihin baya, da alama wannan diramar da ke faruwa na nuna alamun faruwar irin haka a Birtaniya.
A taƙaice ana iya cewa Amurkawa sun ji daɗi matuƙa ganin cewa Yarima Harry da matarsa sun zaɓi su koma Amurka da zama bayan sun samu ƴancinsu.
Ƙasar da ke da akwai ƴanci wato Amurka, wuri ne da ake ganin kowa zai iya sama wa kansa abubuwa iri-iri ba kamar wani Birtaniya ba, da ke da tsarin matsayi-matsayi ba.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da nuna tausayi ga Harry da Meghan a Amurka, tuni wasu labarai da aka rinƙa wallafawa misali a Wall Streer Journal da Politico suka fara magana a kan ma'auratan sun cika ƙorafi.
Idan ma'auratan na so su riƙe soyayyar da Amurkawa ke yi musu, akwai buƙatar su ƙara gaba daga labarin da suke bayarwa na musguna musu zuwa wani labarin daban.
Akwai buƙatar su bayyana irin abubuwan da suke ganin za su iya yi amma aka hana su a matsayinsu na ƴan gidan sarauta











